Nasarar Zaɓen jihar Osun Yana Da Alaƙa Da Gudunmawar Matasa -Bishir Sani Dogo
Daga Abu Ahmad, Katsina
Haziƙin matashin ɗan siyasa kuma Bakanike da ke jihar Katsina Bishir Sani Dogo ya bayyana cewa rawar da matasa suke taka a zaɓen jihar Osun ta taimaka gaya wajan samun nasarar jam’iyyar PDP a zaɓen da aka gudanar ranar asabar ɗin da ta gabata
Matashin ya yi wannan kalamai ne jim kaɗan bayan hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana Sanata Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.
Bashir Sani Dogo bayan kasancewar sa Bakanike ɗan siyasa ne mai aƙidar matasa su tashi tsaye su nemi na kansu sannan su shiga siyasa a dama da su , musamman jam’iyyar su ta PDP a kowane mataki.
Haka kuma matashin ya ƙara jan hankalin matasa da cewa su cigaba da shiga al’amurran siyasa ana damawa da su, domin su ne shuwagabannin gobe.
Ya ce ko shakka babu, matasa sun yi ƙoƙari a zaɓen jihar Osun wanda ya ce sun taimaka ta hanyoyi daban-daban da suka haɗa da bin doka da oda da kuma baiwa jami’an tsaro goyon baya domin gudanar da aikin su.
“Baban darasin da zaɓan jihar Osun ke nunawa shine nasara na tafe a jam’iyyar mu ta PDP a sauran zaɓubuka da ke tafe, wanda ake buƙatar sa hannun matasa da ake kira ƙashin bayan al’umma.” Inji shi.
Da ya juya akan matasan jam’iyyar PDP na jihar Katsina Bashir Sani ya yi kira da su tashi tsaye wajan koyan sana’o’i musamman ayyukan hannu kamar Kanikanci da walda da sauran ayyuka wanda ya ce suna da rufin asiri ba kaɗan ba.
Kazalika ya jan kunnen matasa da kadda su kuskura su yi watsi da sana’ar da suke yi domin hidimar siyasa, su yi amfani da damar su, su yi siyasa mai tsafta wacce ake ganin haske a wannan yanayin.
Bishir Sani Dogo ya yi wani albashir da cewa abubuwan da suka faru a zaɓen jihar Osun alama ce da ke nuna jam’iyyar PDP zata dawo akan karagar mulki a shekarar 2023 a jihar Katsina da kuma ƙasa baƙi ɗaya.
Daga ƙarshe ya yi bayanin cewa nan gaba kaɗan za su fara shirya tarurruka domin cigaba da faɗakar da matasa mahimmanci shiga harkokin siyasa mai tsafta da kuma yin riƙo da sana’o’in hannu domin dogaro da kai.
