September 18, 2026

Ɓarayi Sun Wawashe Kayayyakin Wata Makarantar Firamari A jihar Zamfara

0

Wasu mutane da ba a san ko wanene ba sun yi dirar mikiya a makarantar firamari ta garin Ɗanjibga a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara inda suka wawashe komi na makarantar.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne ɓarayin suka kai wannan samamaye inda suka cire rufi da tagogi da ƙyauran makarantar baki daya wanda haka ya hana ɗalibai komawa makaranta domin ɗauka darasi

Sai dai kuma faruwar hakan ke da wuya sai al’ummar garin suka garzaya domin sanar da hukumar bada ilmin bai ɗaya ta ƙaramar Hukumar Tsafe (SUBEB) da kuma hukumar bada ilmin bai ɗaya ta ƙasa (UBEC) da ke birnin Gusau.

Sanar da hukumomi halin da wannan makaranta ta shiga ya sanya mahukunta sun ɗauki matakin fara binciken yadda al’amari ya faru, ta hanyar ziyartar garin Ɗanjibga da ke karamar hukumar tsafe domin ganewa idanunsu irin ta’asar da aka tabka, Popular News Hausa ta ruwaito

Kazalika masana na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da wannan ɗanyen aiki da suka ce akwai sakaci na hukumomi da kuma mutanen gari.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *