Abu Ne Mai Muhimmanci Ku Mallaki Katin Zabe — Shugaban Karamar Hukumar Danmusa.
An yi kira ga al’ummar karamar hukumar Danmusa da basu da katin zabe kuma sun cika sharuddan mallakar shi da su je, su yi rijistar katin zaben na dindindin.
Shugaban karamar hukumar Danmusa dake jihar Katsina Sanusi Dangi Abbas ne ya yi wannan kiran.
Kamar yadda ya bayyana ta hanyar katin zabe ne mutane za su iya zaben shugabanni na gari.
Ya gode ma Allah SWA bisa samun saukin matsalar tsaron dake damun yankin karamar hukumar ta Danmusa duba da matakan da suka dauka, tare da rokon Allah ya ƙara kawo saukin matsalar tsaron a karamar hukumar dama jiha baki daya.
