September 18, 2026

’Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Bikin Cikar #EndSARS# Shekaru Biyu.

0

Jami’an ‘yan sandan jihar Lagos sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar bikin cika shekara 2 da yin zanga zangar EndSARS a Lekki Tollgate.

A cikin wani faifan bidiyo, an ga masu zanga-zangar suna gudu don tsira da lafiyarsu, kuma hotuna sun nuna yadda aka kama mutane da dama a wurin da lamarin ya faru.

Mai zanga-zangar ya fito ne da safiyar wannan Alhamis ɗin karkashin jagorancin fitaccen mawakin nan Falz da Macaroni domin gudanar da tattaki cikin lumana a babbar kofar shiga Lekki domin tunawa da harbe-harbe da aka yi a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard ta bada rohoton cewa, an tsara gudanar da tattakin tunawa da zanga-zangar #EndSARS# cikin lumana, kafin lokacin da jami’an sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar daga wurin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *