‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda A Enugu.
‘Yan bindiga sun kai hari ofishin’ yan sanda na Inyi da ke Oji River a jihar Enugu, tare da kashe akalla dan sanda 1 da kona ofishinsu.
Yan bindigar sun kashe fararen hula biyu a lokacin harin.
An bada rohoton cewa, ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar jiya Lahadi da safe.
Yan bindigar da suka kai hari kan ofishin yan sanda na Inyi, an ce suna rare wakokin cewa, “babu zabe a kasar Biafra”, tare da ci gaba da munanan ayyukansu.
Wani faifan bidiyo da ke yawo jiya Lahadi da yamma, ya nuna yadda ginin ofishin yan sandan ke ci da wuta, hadi da wasu mutane 2 kwance a cikin ofishin yan sandan.
An ce, an gane wasu muryoyin da aka ji cikin faifan bidiyon, inda aka tabbatar da cewa 1 daga cikinsu dan sanda ne da ke aiki a ofishin.
Mazaunin yankin da ofishin ‘yan sanda ya ke ya tabbatar da harin.
“Na samu labari daga yankinmu cewa, awanni kadan da suka gabata yan bindiga sun kai ma ofishin yan sanda hari da ke yankin, tare da kashe dan sanda 1. Kuma ya zuwa yanzu banda cikakken bayani”, kamar yadda majiyar ta bayyana.
A wani labarin kuma, ana rade-radin akan kafafen sada zumuntar zamani a garin Enugu cewa, yan ta’addan za su yi dawowa kai hari a yankunan Inyi, Achi, Ufuma, Umunze, Ajari da kuma Arondiizogu.
Kakakin shugaban ‘yan sandan kasar Enugu, Daniel Nuskwe, har yanzu ya amsa amsar sanya shi a kan lamarin.
