‘Yan Bindiga Sun Kashe DSP Da Insfekta a Imo.
Yan bindiga sun kashe mataimakin sufuritenda na ‘yan sanda da kuma insufeto da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Umuna yankin Onuimo a jihar Imo.
An bada rohoton cewa, wasu yan bindiga ne cikin mota kirar Hilux baka sanye da kakin sojoji suka kashe yan sandan tare da rugawa a lokacin da suke aikin binciken ababen hawa bakin ofishinsu.
Hakazalika an bayyana cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin yayin da wasu masu ababen hawa suka yadda motocinsu, tare da rugawa domin tsira da rayukansu.
Kamar yadda majiyar ta bayyana, jami’an yan sandan na aikin binciken ababen hawa ne da safe. Basu lura ba ashe mutanen da ke cikin Hilux ɗin yan ta’adda ne sanye da Kayan sojoji. Nan take suka buɗe masu wuta, tare da kashe DSP 1 da insufeto 1. Kuma daga karshe suka ruga.
Ya kara da cewa, lamarin ya haifar da tashin hankali yayin da masu ababen hawa suka yi gaggawar barin motocinsu tare da rugawa domin tsira da rayukansu.
Sai dai, kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Imo, CSP Michael Abbattam, bai samu amsa kiran waya ko sakon tes da wakilin jaridar Popular News Hausa ta Sunnews na.
