Bikin Maulidi: Zawiyyoyi 20 Sun Amfana Da Tallafin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami (Mai Raba Alheri)
Ɗan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya raba kayayyakin abinci ga wasu Zawiyyoyi 20 domin yin hidimar Mauludin Annabi Muhammad (S)
Tallafin dai na da nufin bada tasa gudummawa wajan ƙara inganta hidima ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam da aka saba yi duk shekara.
Haka kuma kayayyakin abincin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa 30 da buhunan Fulawa guda 40 sannan Zawiyyoyi 20 ne suka amfana da wannan tallafi.
Tun da farko da yake jawabi a wajan taron miƙa wannan tallafi, mai baiwa gwamna shawara a ɓangaren Ɗariƙa, Hon. Bishir Ɗan Gambo ya nuna godiyar sa go Hon. Sani Aliyu Ɗanlami bisa ƙoƙarin sa na yin hidima ga Annabi Muhammad (S)
Kimanin shekaru bakwai ke nan Hon. Sani Aliyu Ɗanlami yana gudanar da bada wannan tallafin, saboda haka ba anan ya tsaya ba akwai karin wasu tallafin wanda yake sa ran za’a sake badawa a lokacin zagayen Mauludi na gar baki ɗaya ” inji shi
Da yake na shi jawabin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya ce wannan abin da ake gani yanzu abu da aka sani yi kuma za a cigaba da yin sa a duk lokacin da wannan hidima ta kama domin karfafa soyayyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam.
Hon. Sani Aliyu wanda ya samu wakilcin Sakataren ilmi na ƙaramar hukumar Katsina, Alhaji Mannir Yahaya ya ce Hon. Sani Aliyu ya so halartar wannan mahimmin taro amma saboda wasu ayyuka da suka sha gabansa yasa bai samu damar zuwa ba.
Daga karshe ya godews Malaman Zawiyyoyin da suka amsa wannan gayyata, yace Hon. Yace a basu tabbacin cewa hidimar su a koda yaushe babu gudu babu jada baya, tsaye yake akai, ya yi addu’a Allah ya maida su gidajen su lafiya.
Sai dai kuma a nashi ta’alikin shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Katsina Alhaji Ibrahim Saulawa ya bayyana farin cikin sa da wannan abin alheri da mai raba alheri ya yi musamman a wannan gaɓar ta bukukuwan Mauludi na fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama
Ya ƙara da cewa yana bada tabbacin akan Hon. Sani Aliyu Ɗanlami cewa jami’yyar APC na alfahari da mutane irin sa wajan fitar da Jami’yyar kunya akan duk wani abu da ya shafi al’umma balanta kuma murnar samun fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam
