Yan Bindiga Sun Kwace Bindigun Yan Sanda, Tare Da Kashe Dan Chana A Ebonyi.
Wasu ‘yan bindiga sun kwace bindigun wasu ‘yan sanda tare da kashe wani dan kasar Chinar da suke gadi a wurin hakar ma’adinai da ke Iboko a karamar hukumar Izzi ta jihar Ebonyi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu rundunar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.
“Ba a tabbatar da hakan ba, amma ku yarda da ni, zan tabbatar da hakan gobe,” in ji Anyanwu.
Shugaban karamar hukumar Izzi Mr. Steve Emenike ya bayyana kisan a matsayin abin kunya.
Emenike ya bayyana cewa, mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne sun zo ne a kan babura.
Ya ce karamar hukumar ta sake kafa wata babbar kungiyar ‘yan Vigilante tare da haramtawa babura aiki tsakanin karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safe a yankin.
“Muna aiki tukuru don gano musabbabin lamarin kuma muna aiki tare da jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da DSS don gudanar da bincike kan lamarin da kuma tabbatar da ganin an gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
“Mutanenmu suna cikin zaman lafiya, ba za mu amince da rashin tsaro ba.
Shaidun gani da ido da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce ‘yan bindigar sun kwace bindigun ‘yan sandan da ke gadin ‘dan Chinar a lokacin harin.
“An ajiye gawar wadanda aka kashen a dakin ajiye gawa na Abakaliki,” in ji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya a Jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta wayar tarho cewa, rundunar yan sandan jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba a ranar Lahadin da ta gabata, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
