September 17, 2026

Shugaban Hukumar Kwastam Ya Nuna Damuwa Kan Tara Kudin Haraji Na Tiriliyan 3.

0

Shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Kanal Hameed Ali mai ritaya ya ce hukumar na iya fuskantar kalubale wajen cimma burinta na samun kudaden shiga na naira tiriliyan ₦3.019 na shekarar 2022.

Shugaban hukumar ya ce hukumar za ta samu akalla dala biliyan 17.6 bayan kammala ayyukan ta nan da wasu shekaru, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Ali ya bayyana hakan ne wajen taron tattaunawa na shugaban kasa karo na 55 da tawagar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta tattara tare da aika kudi har naira tiriliyan 2.143 a cikin asusun gwamnati.

Kamar yadda ya bayyana, badakalar hukumar Kwastam na karbar harajin sadarwa wanda aka warware kwanan nan zai shafi abin da ake bukata.

Ya bayyana cewa hasashen da aka yi na tara naira tiriliyan N3.019 ya ta’allaka ne da tunanin cewa ma’aikatar za ta fara tattara kudin ne daga farkon shekara.

Ya ce tsaida kudin harajin kamfanonin sadarwar da aka sasanta a baya bayan, zai zama kalubalen cimma kudurin tara kuɗin shigar da ake son cimma.

Ya ce samun jinkiri wajen amsar kudin harajin kayan sha irinau lemu zai iya bada wata matsalar.

Shugaban hukumar ya ce bada jimawa aka fara tattara kudin haraji, wanda ya yi nuni da cewa yana cikin abinda ake son cimmawa na shekarar 2022.

Ali ya kuma bayyana cewa, Ma’aikatar za ta samar wa kasar kusan dala biliyan 17.6 idan aka kammala.

Ya yi hasashen cewa hukumar kwastam za ta bukaci dala biliyan 3.5 don daidaita ayyukanta gaba daya tare da takaita huldar mutane.

Da yake amsa tambayoyi kan kokarin da yake na kawar da ma’aikatan hukumar daga cin hanci da rashawa, shugaban hukumar ya bayyana cewa an kori sama da jami’ai 2,000 daga aiki bisa rashin da’a da sauran laifuka tun lokacin da ya karbi ragamar shugabancin hukumar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *