Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Babban Dila A Lagos.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta sake bankado wani mai safarar miyagun kwayoyi a Lagos tare da kwato magungunan da kudinsu ya kai naira ₦8,860,000,000.
An gano magungunan ne a gidajen mutumen da ake zargin hamshakin attajiri ne da ke sayar da kwayoyi mai suna Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia da ke rukunin gidaje na Highbrow, Victoria Garden City a unguwar Lekki da ke Lagaos, inda jami’an hukumar NDLEA suka kama kwayoyin na tramadol 225mg da darajarsu bata gaza 13,451,466 ba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA Femi Babafemi ya fitar, ya ce “ kama Ugochukwu, wanda shi ne Shugaban Kamfanin Autonation Motors Ltd na zuwa ne watanni biyu bayan da hukumar NDLEA ta gano wani kamfanin haɗa magunguna a gidan wani dilan kwayoyi a unguwar mai suna Chris Emeka Nzewi, wanda aka kama shi a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli, tare da wani sarrafa masa kwayoyin mai suna Sunday Ukah. Akalla kilogiram 258.74 na crystal methamphetamine da wasu sinadarai da aka yi amfani da su wajen samar da maganin mai guba aka gano su a gidan na Nzewis a lokacin da aka kama shi, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.
“Biyo bayan samun bayanan sirri, jami’an hukumar NDLEA a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, sun kai samame a Plot A45 Road 2 gidan wani dilan kwayoyi mai shekara 52. Binciken da aka yi a gidan ya bada damar gano katan 443 na tramadol hydrochloride 225mg, wanda ke dauke da kwayoyin maganin 13,451,466, yayin da wasu kwalayen tuni suka kone a wata gobara da ta tashi kafin kama shi. Ugochukwu wanda ya fito daga karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra, yana cikin jerin masu sa ido a hukumar a matsayin daya daga cikin masu safarar miyagun kwayoyi na tramadol a Najeriya. Binciken farko ya nuna cewa yana da gidaje kusan shida, kuma daya daga cikinsu yana ajiye kwayar tramadol, yayin da yake zaune a daya a Plot Z-130 Road 67, daya kuma a matsayin ofishinsa. An kuma gano wasu manyan motoci guda biyar a cikin wasu gidajen nasa guda biyu, daga cikinsu an yi nasarar kwashe motoci kirar SUV guda biyu ciki har da wata mota kirar jeep mai da bata jin bindiga.”
Da yake tsokaci akan kamen da aka yi, Shugaban hukumar NDLEA Brig. Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an tsaron da suka gudanar da aikin bisa jajircewarsu, sannan ya kuma yaba wa ‘yan Najeriya bisa yadda suke mara wa hukumar baya a aikinta na kawar da kasar nan daga matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi.
