September 17, 2026

Mutane 3 Sun Mutu, An Kone Motoci 20 Lokacin Da Ake Ma EFCC Zanga-Zanga Don Ta Kama Yan Damfara.

0

Wani tashin hankali ya mamaye wasu sassan jihar Delta, musamman ma Warri, cibiyar kasuwanci ta jihar, da Ughelli, bayanda da wasu fusatattun matasa suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kama wasu da ake zargin masu damfarar yanar gizo ne da aka fi sani da ‘yahoo boys’ da jami’an da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa suka yi. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi barna a kan titin Otovwodo na hanyar Gabas/Yamma, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa, lokacin da ƙurar zanga-zangar ta lafa, an ga akalla mutane uku sun mutu kwance kasa, sannan an kona motoci sama da 20 makare da man fetur.

Masu zanga-zangar dai sun kunna wuta akan Shataletalen Effurun kuma suna dauke da kwalaye masu rubututtuka daban daban kamar irin su “#EndEFCC” a safiyar ranar.

An bada rohoton cewa, zanga zangar ta fara ne a daidai mahadar Otovwodo, Ughelli inda zanga-zangar #EndSars ta fara wadda ta yi muni a Najeriya.

Zanga-zangar ta #Endsars ta fara a irin wannan yanayi na nuna adawa da zaluncin ‘yan sanda da cin zarafin matasa.

Zanga zangar ta wannan Talata wacce ta rikide zuwa zubar da jini da rana ta zo ne kwana guda bayan da jami’an hukumar EFCC na shiyyar Fatakwal, suka kama mutane casa’in da biyar da ake zargi da aikata damfara akan yanar gizo a Warri, jihar Delta.

An kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis, 29 ga Satumba, 2022, a wani samame da aka kai musu a Adesa Ughonton da Jedda na Warri, jihar Delta, bisa zarginsu da aikata zamba akan yanar gizo, a cewar kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujeren.

Matasan da ke zanga-zangar a Warri da Ughelli sun yi zargin cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana su a matsayin masu damfara akan yanar gizo ba tare da wata kwakkwarar hujjar da za ta kare maganarsu.

Daya daga cikin masu zanga-zangar da ya bayyana sunansa Johnson ya ce, “Muna son zaman lafiya a Najeriya, kuma suna amfani da hukumar EFCC wajen kawo cikas da hana matasa kada kuri’a a zaben 2023, kuma ba za mu amince da hakan ba.”

Wani mai zanga-zangar da ya bayyana sunansa da Chiristian ya ce, “Ayyukan hukumar EFCC na neman wuce gona da iri, ba mu da hanyoyi masu kyau, makarantu suna yajin aiki, idan ma mun kammala karatu, babu ayyukan yi, kuma hukumar na kama mu.”

Wani dattijo ma ya ce, yau sai ace bera ya gudu da kudi, gobe ace, sauro ya tashi da kudi, da dai sauransu.

Da yammacin wannan Talatar dai, an ake tawagar sojoji da ‘yan sanda zuwa wurin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *