Kasancewata Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Funtuwa Da Ɗandume Abun Alfahari Ne Ga Matasa Cewar Barista Abubakar
Daga Hussaini Yero, Funtua
Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Mai wakiltar Kanana hukumomin, Funtuwa da Dandume, abun Alfahari ne ga Matasa.
Barista Abubakar ya bayyana haka ne a wajan taron zagayan Maulidin Manzan Allah (saw) na bana a Karamar hukumar Funtuwa.
” Dan Takarar Majalisar Tarayya ya kara da cewa, zaben sa da ‘Yan Jamiyyar APC , su kayi na zama Dan takarar su a babban zabe maizuwa , abun alfahari ne ga Matasa musamman yadda ya ke Matashi sun zaboshi domin suna da tabbacin zayyi masu wakilcin da ya dace da su da yardar Allah, idan na samu nasara a zaben maizuwa, zan dora daga wanda na gada wajan ayyukan cigaba da talafawa Matasa. Inji Barista Abubakar.
” Barista Abubakar ya daulawashin tabbatar da rayuwar Matasa ta inganta, akan haka ne yayi kira ga Matasan da su kauce wa bangar Siyasa da Shaye Shaye. duk Dan Siyasar da ya nemi suyi haka to su bayyana masa cewa, ya kawo Dansa ko Wani nasa. Inji Barista Abubakar.
Da ya koma kan batun Maulidin Manzan ( Allah) Barista Abubakar yayi kira ga mahalarta taron zagayan Maulidin da suyi koyi da kyawawan halayan Mazan Allah dan samun cira ranar gobe alkiyama.
