September 18, 2026

Tsakanin Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jihar Katsina Da ‘Yan Jaridu

0

Daga AK Jani, Katsina

Na kalli faifan vedio dake yawo na Wani da rundunar yansanda ta gurfanar da ake zargin aikata laifi Wanda wannan da ake zargi yake musanta zarge zargen da ake mashi.

Naji Kuma yanayin tambayoyin kwalailaicewa da wasu daga cikin abokanan aiki sukeyi.

To da farko dai bana kallon laifin rundunar yansanda na baje kolin wadanda ta kama bisa zargin laifuka daban daban domin kusan hakan ya zama dole tayi yanzu duba da maganganun mutane na cewa basu komai to kila wannan na cikin matakai data dauka domin nunawa duniya irin kokarin da takeyi duk da wasu masana kundin Mulki sunce hakan ya saba ma doka.

To amman irin yadda ake baje kolin wadanda ake zargin shine abun tambaya da kuma irin tambayoyin da ake masu Wanda ya kamata a ce a kotu ne ya kamata ayi haka. Ance shari’a sabanin hankali domin kuwa lokuttan daban daban ana korafin Yan sanda sun kama wasu da suke zargi an baje kolin su ga yan jarida sun yada an kaishi gaban kotu amman Kuma an sake shi saboda kila an sameshi bashi da laifi a dayan bangaren Kuma gashi can faifan vedio shi nata yawo da sunan an kama shi kuma ba kasafai mutanen mu suka fiye gane banbancin tuhuma da Kuma yanke hukunci ba.

A dayan bangaren suma wasu daga cikin Yan jarida a iya cewa sun sauka daga ainahin aikin su ya Allah ko saboda rashin kwarewa ta aiki ko kuma inda aka raja’a domin zaka ga mafi akasarin kwaikwayon abun da Yan uwansu sukai sukeyi yasa suke barin taiki suna bugun jaki.

Nasan a doka ta aikin Jarida akwai ire iren mutanen da ake zargi da Yan jarida bai kamata bama su bayyana fuskokin su to amman yanzu zakaga yadda ake baje kolin su duk da dai hakan yafi faruwa a kafafen Sada zumunta.

MAHANGA TA.

Ya kamata rundunar yansanda ta kama wadanda take zargi to a dunga bayyanawa ko dai a rubuce ko kuma a dunga takaita tambayoyi manema labarai garesu har sai zuwa lokacin da kotu ta tabbatar da laifin mutum ko kuma ta wanke shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *