Idan Aka Ci Gaba Da Kai Hare-haren Ta’addanci, Za Mu Nemi Mutanenmu Su Mallaki Bindigogi – Akeredolu.
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya sha alwashin umartar ‘yan jihar da su samu bindigogi domin kare kansu idan har aka ci gaba da kai hare-haren ta’addanci a jihar.
Akeredolu ya kuma sha alwashin cewa gwamnatin sa za ta kakkabe masu aikata laifuka daga maboyarsu a fadin kananan hukumomi 18 dake cikin jihar, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da yake bada da tallafin Motoci 50 na sintiri ga daukacin hukumomin tsaro a jihar a wani bangare na kudirin gwamnatinsa na ƙara karfafa tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Ya ce “Kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne suka fi ba fifiko.
Ya bayyana cewa“ idan abun ya gagara da kansu za su nema wa al’ummar jihar bindigogi don kare kansu.
Gwamnan ya ce “koko so ake su zauna cikin gida a ci gaba da kashe su”.
Ya ce wannan muhimmin batu ne, ba zasu yadda a ci gaba da kashe su. Hakan ma ne yasa suke tattauna da masu rike da sarautun gargajiya.”
Gwamnan ya ce idan har ‘yan ta’adda za su iya ƙwatar mutanensu daga hannun gwamnati kuma gwamnati ba za ta iya tsare mutanenta daga ‘yan ta’adda, akwai matsala. A cewar gwamnan anan cikin babbar matsala a kasar duba da yadda yan ta’addan ke yin garkuwa da mutane da dai sauransu.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, “Har yanzu basu manta da mugun aikin da aka yi a watan da ya gabata, lokacin da wasu ‘yan ta’adda da suka kashe mutane a cocin St. Francis Catholic Church, a garin Owo.
