September 18, 2026

Zulum Ya Raba Gidaje 259 Da Tallafin Miliyan 110 Ga ‘Yan-sanda A Jihar Borno

0

Daga M. Shamsudeen, Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis a Maiduguri, ya bayyana cewa gwamnati ta ware gidaje 259 tare da tallafin naira miliyan 110m ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke jihar.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da bankin yan -sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank).

An samar da wannan bankin Microfinance ne domin gudanar da hada-hadar kudi don tallafa wa wajen yin kanana da matsakaitan sana’o’i ga iyalan yan- sanda, yan uwansu tare da kuma al’ummar jihar Borno.

Bukin bude sabon bankin a birnin Maiduguri ya samu halartar babban Sufeto Janar ‘yan sandan Nijeriya, IGP Usman Baba Alkali.

Kafin kaddamar da taron, Zulum ya bayyana cewa raba wa yan-sanda gidaje sama da 259 an yi shi ne sakamakon biyan gwamnatin jihar diyya kan yadda gwamnatin ta yi amfani da wasu filaye mallakar ‘yan-sanda, domin bunkasa abubuwan more rayuwa a babban birnin jihar.

Bugu da kari kuma, dangane da tallafin naira miliyan 110 da gwamnatin jihar ta ware, ya kunshi kashi 50% na kudin; daidai da N55m, gudunmawar jihar Borno ce wajen zuba hannun jari da nufin bunkasa ayyukan bankin a matakin farko.

Sauran naira miliyan 55 kuma, Gwamna Zulum ya ce za a yi amfani da su wajen tallafa wa iyalan jami’an ‘yan sanda ta hanyoyi biyu, wanda abu na farko, shi ne za a yi amfani da naira miliyan 25 don raba wa iyalan ‘yan-sandan da suka mutu a bakin aiki.

Yayin da Zulum ya bayar da umarnin ajiye kudaden a asusun ajiyar yaran da jami’an ‘yan-sandan da suka mutu suka bari. Sannan kuma sauran naira miliyan 30, za a saka su a asusun ajiyar kudi domin tallafa wa matan ‘yan-sanda da ke aiki a fadin jihar Borno.

Har wala yau, Gwamna Zulum ya yabawa shugaban rundunar Yan-sandan Nijeriya, IGP Alkali bisa kaddamar da reshen bankin a Borno wanda ya ce, ya nuna yadda IGP ya ba da fifiko ga jin dadin ‘yan-sanda.

A nasa jawabin, Babban Sufeto Janar na ‘yan-sandan Nijeriya, Usman Baba Alkali, ya yaba da cikakken goyon bayan da Gwamna Zulum yake bai wa rundunar yan-sandan Nijeriya a matsayin abin alfahari.

“Mai Girma Gwamna, za mu yi amfani da wannan dama wajen jinjina maka tare da mika godiya bisa irin goyon bayan da rundunarmu a jihar ke samu na yin aiki yadda ya kamata wajen yakar miyagun laifuka. Ina sane da cewa Borno ita ce jiha daya tilo wadda bayan ta samu motocin yaki guda shida ta mika su ga ‘yan-sanda. Wannan abin a yaba ne kuma ayi alfaharin gaske dashi saboda yadda kuka dauki mana wasu wahalhalu, domin gudanar da aikin tsaron kasa.” In ji IGP.

IGP Alkali ya samu rakiyar shugaban hukumar kula da kananan bankuna ta Nijeriya, Mista Azubuko Joel Udah, da manajan darakta na bankin Mista Akin Lawal tare da manyan jami’an rundunar yan-sanda, hadi da manyan kusoshin gwamnatin jihar Borno tare da Gwamna Zulum a taron.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *