September 19, 2026

Rundunar Yan Sandan Katsina Ta Kama Mai Shake Mutane Da Kebil Don Amshe Masu Mashin.

0

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina SP Isah Gambo ya fitar.

Daga cikin yan ta’addan da aka kama akwai wani Yahaya Muntari mai shekaru 23 dake kauyen Ruma cikin karamar hukumar Batsari wanda ya kware wurin lallasar yan achaba zuwa unguwannin da ba mutane sosai don amshe masu babura.

Kuma yan sandan dake sashen yaki da Kauraye ne suka samu nasarar kama shi a ranar 5/06/2022 da misalin karfe 10:00PM lokacin da suke aikin sintiri akan hanyar Batsari kusa da gidan telebijin Na KTTV bayanda ya lallashi wani dan achaba mai suna Abdullahi Bello dan kimanin shekaru 22 dake kauyen Dantsauni cikin karamar hukumar Jibia da sunan zai kai shi wani wuri kuma ya yi amfani da kebil na mashin ya shake mashi wuya don samun damar kwace mashi babur.

Cikin dan lokaci jami’an yan sanda suka cece shi, tare da kai shi zuwa babbar asibitin Katsina.

Sannan wanda aka kaman ya amsa cewa, ya kashe mutane da dama ta irin wannan hanyar, tare da lissafo sauran yan tawagarsu da suke aikata irin wannan laifin da suka hada da Abubakar Musa wanda aka fi sani da Abu-Abu mai shekaru 17 da haihuwa dake unguwar Abba Jaya, sai Zaharaddini dan shekaru 25 dake unguwar Tsamiya dukkansu yan cikin garin Dutsinma, karamar hukumar Dutsinma.

Rundunar ta kuma kama wasu masu suna kamar haka: Isah Sabitu da aka fi sani da “Babani” mai shekaru 20 da kuma Idi Salisu Gadi mai shekaru 20 dake karamar hukumar Musawa a ranar 30/05/2022 da kimanin karfe 04:00PM.

An kama su ne bisa zargin kai farmaki su ukku dauke da muggan makamai a gidan wata mai suna Sakina Sanusi dake kauyen Rugar Kusa cikin karamar hukumar Musawa, inda suka yi mata fashin kudi naira N263,000:00K da wayar salula kirar Vivo da darajar kudinta ya kai naira N8,000 mallakin wani mai suna Abdulkadir Adamu, daga karshe kuma suka yi garkuwa da diyarta mai suna Hajara Lawal yar shekaru 18 da haihuwa.

Saidai yan sanda sun ceto ta cikin koshin lafiya.

Har wayau, rundunar yan sandan ta kama wani mai suna Jume Bello dan shekaru 20 dake kauyen Jikamshi cikin karamar hukumar Musawa.

An kama shi ne bayanda wasu mata su ukku da suke zaune a yanki suka kai koke lokutta daban daban a ofishin yan sanda na Musawa cewa, yana shigar masu gidaje tare da yi masu barazana da wuka ya amshe masu kudi, wayar salula da kuma yin lalata da su da tsiya.

A lokacin da ake gudanar da bincike ya amsa yin laifin da kanshi, inda kuma ake ci gaba da gudanar da bincike.

Haka kuma, daga karshe rundunar ta bayyana cewa, ta cika hannunta da wani dansakai mai suna Usman Haruna dan shekaru 23 dake kauyen Ruwan Godiya a ranar 24/05/2022 da karfe 11:30AM bisa zargin hada kai da wasu da suka gudu, inda suka tafi da wani dan achaba mai suna Ibrahim cikin daji suka bige shi har ya mutu, tare da amshe mashi babur.

A lokacin da ake gudanar da bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya hada kai ne da wasu mutane ukku wurin aikata laifin da suka hada Nasiru Ali, Adamu da kuma Sa’adu dukkansu dake kauyen Ruwan Godiya da basu zo hannu ba wurin aikata laifin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *