Muddin PDP Na Son Amsar Ragamar Mulkin Najeriya Cikin Ruwan Sanyi Ta Bai Wa Tambuwal Tikiti, TCO Ga Delegates
Kwamitin yakin neman zaɓen Tambuwal (TCO) ya buƙaci Daliget na jam’iyyar PDP da su yi zurfin nazari tare da amincewa wajen bai wa Alhaji Aminu Waziri Tambuwal kuri’unsu domin ya samu zarafin zama dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar da nufin tunkarar matsalolin da suka yi wa Nijeriya dabaibayi.
Shugaban kungiyar yakin neman zaɓen (TCO), Prince Daniel, shine ya shaida hakan ta cikin sanarwar da ya raba wa ‘yan jarida, ya mai cewa lokaci ya yi da za a haɗa karfi da karfe domin ceto Nijeriya daga halin da take ciki a yanzu tare da zaɓin nagartaccen da zai iya kwato mulki daga hannun APC.
Ya ce, yanzu kan kowa ya waye, an san masu son ci gaba da kuma masu mayar da lamura baya, ya ce, ba sabon labari ba ne yadda abubuwa suka cakuɗe a ƙasar nan, wanda ake buƙatar jajirtaccen shugaban da zai fuskancesu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa.
Daniel yake cewa: “In dai maganar jajirtaccen mutum ake wanda zai tserar da Najeriya daga halin kuncin da take ciki, to ba a buƙatar wani dogon nazari, domin kuwa Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kaɗai zai iya wannan namijin aikin. Domin kuwa kowa ya shaida irin ƙalubalen da ake fuskanta a ƙasar nan.
“Saboda haka akwai buƙatar a fara bayyana jajirtattu irinsu. Kuma hanyoyin maganta matsalolinmu a bayyane suke, inda mafi yawansu ma suna nan rubuce cikin ma’aikatu da dama na gwamnatoci. An gaza aiwatar da su ne saboda saboda gazawar shugabanci.”
Ya ƙara da cewa, “Duk da wannan tarin kalubalen, jam’iyyar PDP ta yi rashin nasara a zaɓukan shugaban ƙasa guda biyu da suka wuce a tsahon shekaru bakwai da suka gabata, yanzu kuwa dama ta samu da za a zaɓi nagartaccen dan takara da zai iya fuskantar jam’iyya mai mulki har ma a samu nasara, wanda Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ne kaɗai zai iya yin wannan namijin ƙoƙarin.”
Ya bayyana dalilansu na son Tambuwal ya zama Shugaban Ƙasa, “Idan ka ɗauke kasancewar Tambuwal na matsayin kwararren lauya, jajirtaccen mai hidimtawa al’umma, haka nan kuma masanin ɓangarorin gwamnati na zartarwa da majalisa. Ya kasance mutum mai nagarta da kyawawan halaye sama da zango biyu da yayi a harkokin siyasa.
Yanzu da kawunan ‘yan Najeriya suka rarraba fiye da ko yaushe, jam’iyyar PDP na buƙatar ɗan takarar da zai zama karɓaɓɓe a kowanne yanki na kasar nan, wanda ya zaga kowanne loko da sako a zamansa na tsohon kakakin majalisar wakilai ta ƙasa. Shi ne zai iya ɗaukar kowanne nauyi na ƙasar nan kamar yadda ya ɗauki nauyin dukkanin ayyukan majalisa ta 7.
“A ɓangaren tsaro kuwa, zai iya fuskantar kowanne ƙalubale, kamar yadda ya yaki na jihar, inda ya saka hannu akan dokar ƙalubalen tsaro, tare da samar da motoci 500, babura 765, gidaje 132 ga jami’an tsaro na ƙasa, ban da man zubawa a ababen hawan da kuma alawus dinsu.
Saboda haka ya fahimci matsalar tsaron ƙasar nan kuma zai yi aiki da masu ruwa da tsaki a lamarin da samar da kayan aiki, domin a yaki abin a faɗin ƙasa gaba ɗaya.”
“Yajin aiki malaman jami’a ya zamo ruwan dare, inda malaman kwalejoji ke shirin bin bayansu. Inda gwamnatin tarayya ta yi biris da harkokin ilmi wanda ya zamo kashin bayan kowanne abu.”
“Saboda haka da zarar ya dare shugabancin ƙasar nan zai kawar da wannan, domin kuwa yanzu haka yana ware kaso 29% ga ɓangaren ilmi a kasafin kuɗin jihar Sokoto.
Dukkanin wasu ƙalubale da ake fuskanta a ƙasar nan, ana buƙatar jajirtaccen shugaba wanda ba zai dinga shugabantar ƙasar daga asibiti ba, wanda Tambuwal yana da kosashshiyar lafiya, kuma bai tsufa ba, domin shekarunsa 56 ne kacal,” a cewar kungiyar.
