Matasa Sun Yi Yunƙurin Hana Ɗan Majalisa Hon. Ya’u Galadima Shiga Jakusko
Daga Muhammad Maitela, Yobe
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe, Hon. Zakari Ya’u Galadima ya gamu da fushin fusatattun matasan yankin sa, inda suka yi ƙoƙarin hana shi shiga garin Jakusko, shalkwatar ƙaramar hukumar, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen fidda-gwani.
Al’amarin ya faru ne ranar talata, a lokacin da matasan suka yi ƙoƙarin hana ɗan majalisar shiga garin Jakusko ya wuce Gashuwa, yankin da yake wakilta a zauren majalisar wakilan Nijeriya.
Wanda su ka fara yin zanga-zanga tare da kona tayoyin a kan titunan da zai wuce tare da yi masa ihun ba ma so, wasu kuma ɗauke da duwatsu suna jifar motocin sa.
Wata majiya a garin Jakusko ta shaida wa wakilinmu cewa, matasan sun ɗauki matakin ne biyo bayan dogon lokacin da ɗan majalisar ya ɗauka bai kai ziyara a yankin nasa ba balle ya san matsalolin da al’ummar da yake wakilta.
“Yau kimanin sama da shekara biyu Hon. Zakari Ya’u Galadima bai leƙa yankin Bade/Jakusko ba, sannan dukan abubuwan da ke faruwa a yankin basu dame shi ba, sannan an sha kai ƙorafi ga na sama domin ya gyara abin ya faskara.
Amma saboda tsabar rashin ta-ido, ya ga lokacin zaɓe ya zo, shi ne babu kunya ba tsoron Allah ya ɗauko ƙafa a sake zavarsa; tunanin sa shi ne ya bayar da kuɗi tare da samun ɗaurin ginɗin gwamnati.”
“Sai dai a wannan karon, jama’a sun gaji da irin wannan baƙin mulki wanda yake yi wa jama’a. Kuma ko da ace ita ma gwamnatin babu yadda za a yi ta tilasta wa al’umma abin da ba sa buqata. Amma idan ya na ganin wannan zai yuwu; ga fili ga mai doki. Kuma matakin da waxannan matasa suka ɗauka saƙo ne zuwa gareshi da waɗanda yake ganin zasu ƙwaci mulkin su bashi.” Ta bakin majiyar.
Bugu da ƙari kuma, shima wani ɗaya daga cikin dattawan Jakusko (ya buƙaci a sakaya sunan shi) ya shaida wa wakilinmu cewa, “Ko shakka babu al’ummar Bade da Jakusko sun gaji da salon wakilcin Hon. Zakari Ya’u Galadima, saboda rashin taɓuka abin a zo a gani saɓanin yadda muke jin takwarorin sa a wasu jihohi suna yi. Wallahi mun gaji da wakilcin sa, kuma matuƙar masu faɗa aji a siyasa da gwamnati suka kafe sai shi, to ko shakka babu jam’iyyar PDP na iya cin kujerar Bade/Jakusko.”
“Saboda haka muna kira ga Mai girma gwamna Buni tare da shugabanin jam’iyyar APC su kawo wa mazaɓar Bade/Jakusko ɗauki jama’a sun gaji da salon wakilcin Hon. Zakari Ya’u Galadima, saboda ya kasa taɓuka komai, sannan uwa uba ayyukansa ya nuna cewa ba zai iya ba, ya dace a canja mana da sabin jini mai ƙwazo.” Ya nanata.
Duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi wajen jin ta-bakin Hon. Zakari Ya’u Galadima ko wani makusancin sa abin ya ci tura; an buga wayarsa sau-shurin masaƙi ba a ɗagawa, tare da tura sakon kar-ta-kwana shima babu amsa.
