An warware Tirka-Tirkar KTSTA Da Kano Line Gobe za Su Fara Aiki
Hukumomi sufuri da jihar Katsina da kuma na kano sun warware tirka-tirkar da ke tsakanin hukumomin guda biyu wato KTSTA da kuma Kano line
Wata majiya daga hukumar KTSTA ɗin ta tabbatar wa da Popular News Hausa cewa gobe asabar ne za a cigaba da yin jigilar matafiya daga jihar Katsina zuwa Kano
Akan haka Hukumar Sufuri ta KTSTA na kira ga abokan huldarta da suzo suci gaba da mu’amalarsu da sashen Sufuri kamar kullum.
