September 18, 2026

Na Bature Nahuce Jigo a Siyasar Zamfara Ya Rasu

0

Daga Hussaini Ibrahim Gusau

Jigo a siyasar jihar Zamfara, kuma Kwamanda yakin samun nasara zaɓe a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Nabature Nahuce, ya Rasu samakaon jinyar rashin lafiya a jiya litinan a asibitin Kano da ya ke jinya.

Nabature Nahuce, na daga cikin Datawan ‘Yan Siyasar jihar Zamfara, kuma jajurtace ne wanda bashi da tsoro wanda a toron siyasar idan ya amshi abun magana to angama dan babu wanda zai dushe jawaban da yayi, ya zamo ciwon ciki ‘yan adawa.

Marigayi Nabature Nahuce, babban Ɗan kasuwa ne da kuma Kwangila a matakin gwamnatin jihohi da na tarayya kafin rasuwarsa.

Jama’a da dama ne suka halarci janaizar sa a Garin Nahuce sake cikin ƙaramar hukumar Bungudo jihar Zamfara.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *