September 18, 2026

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane Biyu Da Suka Kashe Maye.

0

Wata mata dai ce mai cike da takaici ta biya mazan biyu ₦5000 don su kashe wani dattijo mai shekaru 85 da ake zargi da maita a jihar Adamawa, inji majiyar Popular News Hausa ta Vanguard.

Yan sanda sun kama matasan biyu masu suna Gayawan Danzaria mai shekaru 22 da kuma Thank-God Obadia mai shekaru 18 da haihuwa.

An bada rohoton cewa, matar da ta tura su aikin ta ruga.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasan biyu sun kashe mutanen har lahira da gatari bayan da matar da ta gudu ta zarge shi da yin maita.

Matar dai ta zargi mamacin da yin maitar danta.

Obadia ne dai ɗauke da gatari ya tafi da Danzaria gidan marigayin da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Litinin.

Dan Zaria na gadi daga waje, Obadia ya shiga ciki tare da samun dattijon da ke kwance ya daddatse shiga da gatari.

Kuma nan take tsohon ya mutu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Suleman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *