September 19, 2026

Wani Lauya Ya Nemi Kotu Ta Soke Takarar Tinubu Saboda Yin Muslim Muslim.

0

Wani lauya mazaunin Abuja, Osigwe Momoh ya shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya a kan jam’iyyar APC bisa tsaida dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa duka Musulmi a babban zaben shekarar 2023.

A cikin karar, lauyan ya bukaci kotun da ta bayar da umarnin dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) daga buga sunan dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar ta APC, Bola Tinubu bisa zargin karya kundin tsarin mulkin Najeriya.

An bayyana sunan jam’iyar APC a matsayin wadda ake ƙara ta daya, sai Tinubu na biyu, yayinda hukumar INEC ke zama ta ukku.

Momoh, a farkon sammacin ya yi nuni da cewa, bisa ga babi na biyu na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska, dole ne jam’iyyun siyasa su samar da ‘yan takarar shugaban kasa da na mataimakansu daga kabilu da addinai daban-daban na kasar.

Don haka ya nemi a yi la’akari da sashe na 14 (1) da (3), 15 da 224 (a) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi ma shi gyaran fuska, wadanda ake karar sun saba doka, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar AIT.

Ya ce dole ne dukkan jam’iyyun siyasar bisa babi na biyu na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska, su sami ‘yan takarar shugaban kasa da na mataimakansu daga bangarori daban-daban na kabilu da na addinai na kasar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *