September 18, 2026

Abubuwa 10 Da Za a Riƙa Tunawa Da Hon. Salisu Iro Isansi Da Su A Siyasar Ƙaramar Hukumar Katsina.

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Siyasa rigar ‘yanci, wannan shi ne take mafi shahara da ake yi wa siyasa a ƙasar Hausa, wato dai mutum yana da ‘yan cin ya yi ko ya bari, idan zai yi, to ya yi mai kyau mai tsafta, idan kuma ba haka tarihi na nan a madakata

Babu shakka, ƙaramar hukumar Katsina kamar kowace ƙaramar hukuma, ta yi zarra, ta yi fice ta kuma kafa tarihi a siyasa, duba da irin mutanen da suka shugabanci tafiyar da ita a matakin shugabancin ƙaramar hukuma da kuma majalisun dokoki da na tarayya.

Daman haka al’adar take, duk inda za a samu mutun fiye da ɗaya, sun yi abin kirki, lallai sai an samu wanda zai zama zakara a tsakanin sauran, wannan batu haka yake, babu tantanma ko saɓani a babin siyasa

Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya, a shekarar 1999 Hon. Salisu Iro Isansi shi ne mutum na shida da ya samu damar wakiltar ƙananan hukumar Katsina a majalisar tarayya wanda hakan ne ya bashi damar zama zakara kuma gwarzo a siyasa.

Duk mutanen nan biyar da suka shugabanci ƙaramar hukumar Katsina a majalisar wakilai ta tarayyar sun yi bakin ƙoƙarin su, sun yi abinda suke iya sun gama, amma dai har gobe akwai abubuwa da ba su sami damar yi ba kamar yadda Hon. Salisu ya yi amfani da irin da damar da saura suka samu ya kafa tarihi.

Na yi imanin cewa zaki yarda da ni akan abubuwa goma da zan bayyana wanda sune
Hon. Salisu Iro ya yi amfani da su wajan banbanta kansa da sauran ‘yan siyasa da suka taɓa jagorancin ƙaramar hukumar Katsina a majalisar tarayya.

  1. WAKILCI NA ILIMI: Duk wakilcin da aka yi amfani da ilmi wajan aiwatar da shi, yana na daban abin kwatance da za a riƙa tunawa da shi komi tsawon lokaci, babu shakka kowa a ƙaramar hukumar Katsina musamman waɗanda ke biye da al’amaran siyasa zai iya zama shaida game wakilcin Hon. Salisu iro acikin shekaru uku da watanni.

Kasancewar sa mai ilmi na zamani da na addini babu mai musun cewa bai ƙaramar hukumar Katsina bata samu wakilci na gari ba, kuma nasan duk wanda ya waye a duniyar siyasa yana san mai ilimi da aiki da shi a kowane irin al’amari, sai dai idan ana magana ne ta san rai.

Abubuwan da jama’ar Katsina ta tsakiya suke gani daga ɓangaren Hon. Salisu Iro Isansi, ilimi ne jagora wajan samar da su, kuma nasan ko nan gaba, ya bar tarihin cewa Katsina ta tsakiya tana buƙatar mutum irin sa, kuma na tabbatar za a riƙa tunawa da shi akan haka.

Ba sai na yi lissafin abubuwan cigaba da ya samar ba a matsayin sa na ɗan majalisar tarayya ba, abubuwan da za su biyo bayan kammala wa’adin mulkin sa, za su kasance amsa ga wanda bai gane abinda nake faɗa a yanzu ba.

Daga lokacin da aka rasa wani wakili da ya fi shi, kwazo da kaifin basira da ilmi wajan shugantar ƙaramar hukumar Katsina, za a fara tunawa da shi musamman duk lokacin da aka ga ɗaya daga cikin abubuwan da ya yi amfani da ilimin wajan samarwa al’umma da shi

  1. LISSAFI. Lissafin siyasar Hon. Salisu Iro daban yake da na sauran, ina son masu karatu su tuna lokacin da ya samu nasarar cinye zaɓan fidda gwani a shekarar 2018 babu wanda ya yi tunanin haka, to amma Hon. Ya lissafa yadda tafiyar take, cikin hikima da taimakon Allah sai ga nasara.

Yadda yake tafiyar da sha’anin siyasar sa ada da yanzu, kowa yasan acikin lissafinsa kome na tafiya ne da sa hannun masana da kwararru ma su taimaka masa wajan yin wannan aiki, a 2018 ba wanda yake kallon siyasa a wani ma’auni na nasara sai daga baya aka an kare da haka.

Nasan wani zai ce to ina lissafin na shi ya tsaya, a 2022 yana kan kujera amma bai samu nasarar lashe zaben fidda gwani ba, ko bai yi lissafin bane daidai?

Haƙiƙa duk wanda zai yi wannan tambaya yana da amsa, sai dai lokacin faɗin amsar bai yi ba, korafe-korafen da Hon.Musa Yusuf Gafai ya yi sune ƙaramar amsar ga mai tambaya.

Nasan kun gane abinda nake faɗa kuma akan haka ma kuna iya yanke hukunci tare da tunawa da wannan bayan Allah wanda idan muka kira shi da Damo Sarkin Hakuri ba a yi laifi ba.

  1. HUKURI: Hakuri na zama matakin nasara akan kowane al’amari na duniya, wannan ɗaya daga cikin halaye da nagarta da kowane ɗan siyasa ya kamata a ce yana da su, kuma yana amfani da su, hakuri da kauda kai da Hon. Isansi ya nuna a wannan lokaci sun isa darasi ga masu neman mulki na wannan lokaci.

Alal haƙiƙa na jima ban ga wanda saboda hakuri ba, ake cuta masa a siyasa kamar Hon. Salisu Iro Isansi ba, ya yi hakuri iya hakuri sai dai wannan magana ta hakuri ba kowa zai gane abinda take nufi ba da sauri ba, sai ya duba irin gashin kumar da Hon. Iro ya sha a hannun manya sannan sai jinjina masa kuma yi masa fatan alheri.

Wannan kalma ta hukuri na jinginawa Hon. Isansi ita, ko lokacin da suka ziyarci shugaban ƙasa Muhammad Buhari a gidansa da ke Ɗaura Buhari ga wannan sallar Buhari ya tabbatar da ita akansa gaban taron jama’a, kuma daman an ce mai hakuri yakan dafa dutse har ya sha romansa.

Saboda hakurin sa duk ya samu nasarorin da ake magana akan su, wani abin ban sha’awa game da Hon. Isansi shi ne, baya daukar al’amari a mutu ko ayi rai, wannan ta sa duk labaransa da zaka ji, sai ka ji an ce mutu ne mai kauda kai da hakuri.

  1. SANIN DARAJAR MUTANE: Ta wannan ɓangaren an ce Hon. Salisu Iro Isansi ya gagara duk wanda ya yi mu’amala da shi, baya kuka saboda haka ake yi masa wani kallo na mutum da ya san darajar mutane.

Kazalika samun nasarar sa a siyasa yana da alaƙa ta kusa da irin ƙyakkyawar mu’amalarsa da jama’ar da suke kewaye da shi, alamomi da yawa sun bayyana cewa baya magana biyu, sannan baya jeka ka dawo ba, ba maganar zan jiranka an jima, ko kuma ka kirani lokaci kaza bai amsa ba.

A bisa haka, idan ka ɗora Hon. Salisu akan sikelin mutuncin acikin al’umma sannan zaka iya gane irin asarar da aka tafka sakamakon rashin da za a yi ba tare da cike gurbinsa ba da wani irin sa ko mai kama da shi a siyasar ƙaramar hukumar Katsina ba

Kodayaushe jama’a na san yin hulɗa da mutumin da ya sa daraja da ƙimar mutane, hakan na bada wata dama a fahimci juna cikin lokaci. Sannan a amfani juna daga lokaci zuwa lokaci, in dai kuwa haka ne, ya zama wajibi a riƙa tunawa da wannan bayan Allah.

  1. SIYASA MAI TSAFTA: Duk ɗan siyasar da aka yi wa shaidar cewa yana siyasa mai tsafta, haƙiƙa sai ya riƙa tsorata ‘yan jagaliya, masu yawo da ‘yan daba domin tada hankali akan duk abinda suka ganin za su rasa shi.

Har gobe an kasa samun mutum ɗaya a ƙaramar hukumar Katsina da Hon. Salisu ya yi amfani da ‘yan dabar siyasa ya ci mutuncin sa, sauran waɗanda suka jagoranci Katsina ta tsakiya fa? Na aiko da wannan tambaya ina jiran amsa idan akwai.

Yanayi da tsarin tafiyar da siyasar Hon. Salisu ta sha bamban da ta sauran kamar yadda na faɗa tun a farkon rubutu na, na ce akwai masu kama masa waɗanda masana ne shi yasa ake ganinsa wani na daban. Daman an ce tafiya da gwani mai daɗi amma…..!

Na yi imani da Allah cewa idan da gwamnati da gaske take akan yaƙi da ‘yan dabar siyasa to ta baiwa Hon. Salisu kyautar girmamawa saboda yadda yake tafiyar da siyasar ba tare da ‘yan bangar siyasa ba, kuma da ta haɗa hannu da shi wajan magance wannan matsala. Haƙiƙa ka zama madubin dubawa a wannan fanni kuma ya zama wajibi a riƙa tunawa da kai.

Anan zan ɗan tsaya in huta, kafin in cigaba, kamar yadda na ambata abubuwa goma ne da za a rika tunawa da Hon. Salisu Iro Isansi akan su bayan ya kammala wa’adin mulkin sa a majalisar tarayya.

Ku biyo ni sannan a hankali domin jin sauran abubuwa biyar game da wannan bayan Allah.

Na gode
El-Zaharadeen Umar
Katsina.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *