Zaɓen 2023: Mace ce Da Cikin Ga Manyan Jam’iyyun Siyasa A Katsina
Daga Abdul Jani
Ina ta nazari akan yadda al’amurran siyasa ke faruwa tsakanin manyan jam’iyyu guda biyu na APC da PDP da kuma NNPP da ta kunno kai, itama tana neman ɗarewa madafun iko.
Tun daga lokacin da aka kammala zaɓukan fitar da gwani waɗannan jam’iyyu suka shiga rikici wanda a iya cewa hakan ya zamo alkhairi ga PDP domin ta samu karɓar mutane da yawa waɗanda aka ɓatama rai a jam’iyyar APC, haka itama NNPP ta amshi mutane da yawa musamman ‘yan majalisu na tarayya.
Hakan ya cigaba da zama barazana ga APC duk da dai ita tana ganin mafi akasarin mutanen da suka fita amfanin su ya kare ga jam’iyyar duk da masu sharhi akan harkokin siyasa na kallon hakan zai zama barazana ga jam’iyyar a zaɓen 2023.
A wani ɓangare kuma wasu na kallon muddin APC bata ɗauki matakai na haɗa kan ‘ya ‘yan jam’iyyar ba to zata sha mamaki domin kusan sau ukku jam’iyyar PDP na karɓar dubban mutane da suka bar APC bayan kammala zaɓen fitar da gwani amman har yanzu ba’aga APC ta amshi dubban mutane da suka fice daga PDP ko NNPP ba
Duk da kwamiti da jam’iyyar APC ta kafa domin sasanci a iya cewa kamar har yanzu akwai aiki ja gaban kwamitin domin bayan kafa kwamtin ne aka samu wasu masu rajin a Gyara a APC. Kenan kodai a canza ‘yan kwamitin ko kuma a canza salon da ake tuntuɓar waɗanda ake ƙoƙarin baiwa hakurin.
A nata ɓangaren kuma PDP da take fafutukar ganin ta mamaye ko’ina domin cin zaɓe akwai yiyuwar zata ɗebi kara da kiyashi wanda kan iya zamowa matsala gare ta kafin zaɓe da bayan zaɓe.
Haka kuma waɗannan jam’iyyu suna rige rigen samun goyon bayan tsohon sakataren gwamnatin Katsina Mustapha Inuwa kuma wanda ya nemi takarar kujerar gwamna? NNPP sunje PDP sunje shima Dan takarar gwamna a APC shine ya fara ziyartar shi awanni kaɗan bayan ambata sakamakon zaɓen su.
Shin ya zama jigo ne ga siyasar Katsina da ake rige rigen zuwa wajan shi? Shin sakacin APC ne yasa jam’iyyu ke ganin zasu iya kwace mata mutumin da ya zo na biyu a neman takarar gwamna? Shin idan har sunci nasarar jawarcin shi ya fita daga APC ya zaiyi da yaran shi waɗanda suka samu tikitin takara a APC ?
