Ana Shirin Yi Wa Jam’iyyar APC Ta Jihar Katsina Shigo-Shigo Ba Zurfi.
Daga Abdulrahaman Aliyu, Katsina
Dokar da samar da jam’iyyar APC ta haramta samar da shugabanci a cikin shugabanci shi ya sa aka samar da gurabu na yin kwamitoci da za su taimaka wajen warware matsaloli tare ƙoƙarin magance duk wani abu da ake ganin zai haddasa matsala a cikinta.
Irin wannan ƙoƙarin ne ya haddasa dakile tasirin wasu kwamitoci ko kungiyoyi dake ikirarin gyara a cikin jam’iyyar, misali APC Aƙida da APC a gyara duk mun ga yadda uwar jam’iyya ta yi tsaye wajen ganin an magance su wanda ya haddasa dakatarwa da kuma kora ga wasu daga cikin waɗanda suka samar da waɗannan kungiyoyi.
Kwatsam sai kuma yanzu ga wata makamanciyar irin waɗancan kungiyoyin ta sake bulluwa da sunan wai ‘KWAMITIN SA KAI DOMIN TABBATAR DA HAƊIN KAN JAM’IYYAR APC’. ko shakka babu wannan kwamiti haramtacce ne a kundin tsarin tafiyar da jam’iyya. bisa dalilai kamar haka;
Na farko wani mutum daga wajen shugabancin jam’iyya bai da hurumin kafa wani kwamiti kuma ya sanyo EXCO na jam’iyya sannan ya ba kansa shugabanci kuma da sunan jam’iyya wannan ba daidai ba ne, domin uwar jam’iyya ko kuma masu ruwa da tsaki a matakin koli ne kadai jam’iyya ta aminta da suyi irin wannan kwamiti.
Muna kira ga uwar jam’iyya ta jiha da ta dawo cikin hayacinta, ta kuma gyara shugabancinta, ta daina bari wasu baragurbi kullum na ƙoƙarin raba kawunan ‘ya’yanta.
Hausawa na da wata karin magana da suke cewa shi gyara daga gida ake fara shi, wanda ya gaza gyara gidansa shi zai ce zai gyara gidan wani?
Yana da kyau ɗan takarar gwamnan Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC ya hankalta da ƙoƙarin da wasu ke yi na ganin sun kawo tasgaro a tafiyar jam’iyya da sunan su ‘ya’yan jam’iyya ne amma kuma a gefe guda kwangila suka amsa, duba da cewa ba sa iya tsayuwa da kansu sai sun jingina da wasu.
Mutumin da ya kasa samar da ‘delagate’ ɗaya a ƙaramar hukumarsa, matsayinsa na shugaban yakin neman zaɓen wani ɗan takara, shi ne kuma zai zo ya ce ma wai zai sasanta wasu? Ya fara sasanta kansa da mutanensa mana.
Mutumin da tun ba a yi nisa ba ya fito ya baranta kansa da uban gidansa ya watsa mai kasa a kasuwa shi ne zai ce zai jagoranci sasanta wasu?
Mutumin da ya tara mutane kuma ya kira gwamna ya zo ya sa albarka wajen alƙawarin gina wasu azuzuwa a ƙaramar hukumarsa, amma gwamna na ɗagawa aka watsar da aikin har yau shiru, shi ne kuma zai ce wane an ɓata mai zai gyara shi?
Yana da kyau jam’iyyar APC ta yi karatun ta natsu wajen dakatar da duk wani da zai yi wa uwar jam’iyya katsaladan musamman abin da ya saɓawa doka.
