September 17, 2026

An Fara Bada Horo Akan Aikin Tattara Bayanai Na Shirin BESDA a Katsina.

0

Hukumar bada ilimin bai daya hadin gwiwa da shirin samar da ingantaccen ilimi wato BESDA su ka shirya bada horon.

Ana bada horon ne a dakin taro na Education Resource Centre da ke cikin garin Katsina.

Da yake bude bada horon, daraktan tsare tsare, bincike da kuma kididdiga na hukumar bada ilimin bai daya ta jihar Katsina Mohammed Lawal Kofar Sauri ya bayyana cewa hakan nada nufin ganin ana tattara sahihan bayanai daga kananan hukumomin jihar.

Shugaban sashen santa ido na hukumar Abubakar Abdulhamid ya ce kananan hukumomi 21 da ke amfana fa shirin sun haɗa da Kafur, Funtua, Mulumfashi, Musawa, Katsina da kuma karamar hukumar Batagarawa.

Sauran sun haɗa da Mai’adua, Daura, Sandamu, Dutsinma, Kurfi, Bindawa, Ingawa, Kaita, Kusada, Rimi, Rimi, Kankia, Dutsi, Mashi, Mani da kuma karamar hukumar Charanchi.

Abubakar Abdulhamid ya kara da cewa, ana tsammanin mahalarta horon za su tattaro bayanan makarantun allo, makarantun da kuma tattara bayanan kayan koyo da koyarwa da ake samar masu.

Ya ci gaba da cewa, masu tattara bayanan za kuma su tattaro bayanan na’urorin samar fa wutar lantarki na “inverter” da aka sanya ma hukumomin ilimin na kananan hukumomin, kudin alawus alawus da kuma adadin yaran da ake sanyawa makarantu, da dai sauransu.

An kuma bukaci mahalarta horon su maida hankali kan abinda ake kiya masu.

Wanda suka horon sun yaba ma gwamnatin jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki bisa taimakawa don ganin an samu ingantaccen ilimi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *