September 18, 2026

Shirin AGILE Zai Taimaka Wurin Bunkasa Ilimi Daga Tushe A Jihar Katsina — Yusuf Adamu Barde.

0

Mai garin Barde da ke cikan gundumar Tsiga a karamar hukumar Bakori ya ce aikin gyaran makarantun sikandiren da ke gudana a karkashin shirin nan na bunkasa Ilimi mai suna AGILE zai taimaka wurin bunkasa ilimi tun daga tushe.

Yusuf Adamu Barde ya fadi hakan ne lokacin da yake duba makarantar sikandiren Barde da ake gyarawa.

Kamar yadda ya bayyana, idan aka kula da gyaran yadda ya kamata, zai taimaka ma kokarin gwamnati a bangaren magance matsalolin da ilimi ke fama da su a jihar Katsina.

Ya ce ayyukan da shirin AGILE ke gudanarwa ingantattu ne.

Hakimin ya yi kira ga shugabannin makarantun su gudanar da ayyukan yadda ya kamata.

Shugabannin makarantun na ƙarama dana babbar sikandiren ne suka zagaya da hakimin a lokacin duba aikin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *