September 17, 2026

Gine-gine 3 Sun Sake Ruguzowa A Lagos.

0

Wasu gine gine ukka da ke kan titin Sonuga, Palm Avenue a karamar hukumar Mushin a jihar Lagos sun ruguzo a yau Juma’a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne da karfe 12 na rana ana tsaka d ruwan sama.

majiyar Popular News Hausa ta Vanguard ta bayyana cewa, har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a iya tantance ko gine ginen sun taushe mutane.

Sai dai jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Lagos (LASEMA) da hukumar kashe gobara ta jihar Lagos, sun isa wurin domin yin aikin ceto.

Za ku ji karin bayani nan gaba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *