September 17, 2026

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kashe dan bautar kasa a Abuja.

0

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama wasu mutane uku da ake zargi da laifin hada baki da kuma kisan wani matashi mai suna Terungwa Stephenie, dan shekara 26 mai yi wa kasa hidima da ke Abuja.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ta ce an kama su ne biyo bayan samun bayanan sirri da sashen rundunar mai binciken laifukan kisan kai ya yi.

Jaridar LEADERSHIP ta ce, Mutanen uku da ake zargin sune; Jenifer Tsembe mace mai shekaru 26; Monday Simon (aka Black) mai shekaru 36 da haihuwa, da Solomon Abu, mai kimanin shekaru 35, dukkansu mazauna titin Oguta Lake Street, yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja, kuma bisa radin kansu, sun bayyana cewa suna da hannu wajen aikata wannan danyen aiki. aiki.

Ta kuma ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gaskiyar lamarin, yayinda kuma ake kokarin ganin an cefke wadanda suka gudu da ake zargi da hannu a ciki.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *