September 17, 2026

Me Zauran APC A Gyara Suka Tattauna?

0

A ƙoƙarin da ‘ya’yan zauren APC Agyara keyi domin ganin an samu gyara a cikin jam’iyyar su ta APC

Sun yi zaman gagawa a yau Talata inda mafi yawancin ‘ya’yan zauren suka halarta daga kowace shiyya ta jihar katsina

Zaman na yau sun tattauna irin binchiken da kowanen su yayi da Kuma Kara duba inda matsalolin jam’iyyar suke tareda Neman hanyoyin da za,a samu gyara domin samun nasarar dukkanin zaɓuka masu zuwa a shekara me zuwa

Bayan haka sun maida ofishin shugabar Mata a hannun Hajiya Amina mataimakiyar woman leader ta zauren APC agyara saboda chanjin sheka da Aisha mashi tayi a matsayin ta na woman leader ta koma PDP

‘Ya’yan zauren na APC agyara sun sake jaddada tsayuwarsu a jam,iyyarsu ta APC inda sukache babu gudu babu ja da baya Kuma zasuchi gaba da sasanta yayan jam,iyyar har Allah ya Basu Nasara domin Nasarar APC data jihar katsina itace ke gabansu.

Daga mustapha Ibrahim kofar marusa D,G media 2

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *