September 17, 2026

Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Afuwar Rufe Gidajen Yaɗa Labarai

0

Daga Hussaini Yero

Gwamnatin jihar Zamfara, Karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Bello Matawalle, ta nemi afuwar da rufe kafafen yada labarai na tarayya da masu zaman kansu a jihar.

Mai ba Gwamna Shawara ,Kuma Shugaban kwamitin hukunta Bindiga Masu Garkuwa da mutane Satar Shanu da manyan laifuka na jihar Zamfara, Alhaji Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Gusau.

Kafafen yada labaran da gwamnatin jihar ta rufe sun hada da NTA Frcn’s Pride FM Gusau, Gamji TV, Gamji FM da kuma Al-umma TV masu zaman kansu.

Dokta Shinkafi ya ce gwamnati ta fusata ne bisa zargin karya dokar Majailisar zartarwa mai lamba 10, 2022, wadda ta fara aiki a ranar 13 ga Oktoba da tabgabata.

A cikin wannan oda, gwamnati ta haramta duk wani gangamin siyasa da tarukan siyasa a jihar saboda matsalar tsaro, tare da dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar tare da rufe hanyoyin Kananan hukumomin Anka, Bukuyum da Gummi baki daya da sauran garuruwa da kauyukan da abin ya shafa. ya shafi akan ta oda No 10, 2022.

Shinkafi ya bayyana laifin kafafen yada labaran da abin ya shafa be dan sun karya dokar ta hanyar yada taron Siyasa “ba bisa ka’ida ba” na dan takarar gwamna jam’iyyar PDP, Dr Dauda Lawal-Dare, a Gusau ranar Asabar.

Ya ce “Taron siyasa ba bisa ka’ida ba” ya haifar da tabarbarewar tsaro da wasu matasan jam’iyyun siyasar biyu suka yi, yana mai cewa “’Yan sanda sun tabbatar da cewa an harbe mutum guda tare da jikkata wasu 18 a yayin taron.”

Shinkafi ya kara da cewa, matakin da gwamnati ta dauka na rufe kafafen yada labarai ya janyo cece-kuce daga kungiyoyi da hukumomi daban-daban da ba a taba ganin irinsa ba.

Hukumomin yada labarai,sun hada da hukumar yada labarai ta Najeriya (NBC), kungiyar yada labarai ta Najeriya kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), cibiyar yada labarai ta kasa da kasa (IPI), da dai sauransu, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, tare da yin kira da a gaggauta daukar matakin janye dokar,wace ba bisa kaida ba.

Shinkafi, ya kara da cewa, matakin da Gwamna Matawalle ya yi ya kasance bisa jagorancin ikon sa da kudin tsarin mulki na Kasa ya bashi ,a matsayinsa na Shugaban tsaro na jiha.inji Shinkafi.

“Dan haka rufe kafafen yada labarai an samu kuskure ne wajan bada odar ,Amma dan laifi sunyi shi,dan a gaban wakilan kafafen yada labarai gwamnatin ta sanya dokar inji Shinkafi

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *