September 17, 2026

Babu Ruwan Jami’yyar ADC Da Nuna Ƙabilanci Cewar Hon. Haruna Yahaya

0

Daga Babangida Sunusi, Kano

Ɗan takarar majalisar jiha a ƙaramar hukumar Rogo da ke jihar kano ƙarƙashin jam’iyyar ADC Hon Haruna Yahaya Kadana, ya bayyana irin matsalolin da suka sha gaban ƙaramar hukumar ta Rogo yasa shi kudartar fitowa takara dan nemo hanyoyin da za su bi dan kawo sauyi mai ma’ana ga al’ummar yankin sa.

Hon Kadana Wanda ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai ciki harda Popular News hausa ya yi karin haske kan kudurinsa akan jama’ar sa a makon jiya, inda ya ce lallai ƙaramar hukumar Rogo tana cikin halin rashin wasu ayyukan na more rayuwa a halin yanzu dan haka matsayin sa na matashi kuma mai hangen dama idan ya samu nasara zai kawo chanji mai ɗorewa.

Kadana Wanda ya misalta jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyya mai san kawo sauyi ba tare da duba launi ko wariya ba ga addini ko ƙabila ba yabasu damar dakko ta matsayin jam’iyya mafita ga ‘yan ƙaramar hukumar Rogo da ke jiha har da matakin ƙasa a zaɓe mai zuwa.

Sannan yayi nuni da ɗan takarar kujerar gwamnan jihar kano Malam Ibrahim Khalil da yake jagora ga al’umma kuma shugaba abin koyi, dan haka ko tanan jama’a zasu iya fahimtar lallai tafiya ‘yan takarar ADC babu wasa a tare da su.

Sannan yace lallai lokaci yayi da jama’a za su yi ma kan su hisabi irin na siyasa wajen zaɓen shugabanni dan yi ma su ayyukan da za su kawo cigaba a yau da kullum da rayuwar su, tare da morewa daga wanda suka zaɓa.

Sannan yanzu haka shirin gidauniyar sa na ba mata da matasa jari yayi nisa tare da ba ɗalibai taimako wajen ilimi da sauran al’umma taimako inji Hon Haruna.

Daga ƙarshe ya bayyana wasu garuruwa irin Zoza da Zarewa, Gwangwan da sauran Mazaɓu na Rogo babu wani abu da zai nuna kazo ƙaramar hukumar Rogo banda Sakatariya.

Sai ya ƙara da cewa, akwai bukatar kowa ya samu ya karɓi katin zaɓen sa dan samun damar kada kuri’arsa wajen zaɓen gwanin su da zai kawo cigaba gare su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *