Kungiyar Mun Gani A Kasa Ba Labari Ba Ta Gudanar Da Zama Da Kungiyoyi Daban Daban Akan Yan Takarar APC.
An yi zaman a karamin dakin taro na hukumar ɗaukar ma’aikatan jihar Katsina.
Shugabannin kungiyoyin sun yi zaman ne domin tattauna yadda za a yi tafiya da kungiyoyi wajen ganin Dr. Dikko Umar Radda ya samu nasarar zama gwamnan jihar Katsina, Asiwaju Ahmad Bala Tinubu kuma ya zama shugaban Najeriya a shekarar 2023.
Zaman dai ya samu halartar shugaban matasan jam’iyyar APC na Najeriya Abdullahi Dayo Israel, da sauran mutane maza da mata daban daban.
Kungiyoyin da suka halarci zaman sun haɗa da Kofar Sauri Women Katsina, Tinubu Vanguard, Yar Baiwa Development, Katsina Youth Solidarity Forums, Katsina Cooperative Society, APC youth mobilisation Batagarawa Local Government, Youth progressive for people change (YPPC), da dai sauransu.
Kuma dukkan kungiyoyin sun nuna goyan bayansu ga tafiyar yan takarar jami’ar APC.
