September 18, 2026

Wata Shugabar Makarantar Mata Ta Yaba Ma Shirin AGILE A Dutsi, Jihar Katsina.

0

Shugabar babban makarantar sikandiren mata da ke Shargalle cikin karamar hukumar Dutsi ta bayyana gamsuwa da yadda ake aiwatar da ayyukan shirin AGILE a makarantar.

Binta Baraka Sade ta faɗi hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Dutsi.

Faransifal ɗin da ta yi magana ta bakin mataimakiyarta Fa’iza Shehu Adamu, ta yi nuni da cewa shirin AGILE ya yi ayyuka daban daban a makarantar domin bunkasa ilimi a yankin.

Baraka Sade ta ce, an samar da fanfunan samar da ruwan sha domin samar da isasshen ruwan amfani ga ɗaukacin makarantar.

Faransifal ɗin ta ce an samar kujeru da teburan zama don samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.

Babban jami’in da ke kula da harkokin ilimi tsakanin ɗalibai da hukumar makaranta Malam Nasiru Yusuf Dutsinma da kuma Malam Musa Aliyu sun ce bayan gudanar da ayyukan gyare-gyaren makarantar, an kuma samar da kayan amfanin gida da suka haɗa da keken dinki dana saƙa da kuma tukunyar sanwa ta iskar gas domin koyar da sana’o’i.

Malaman makarantar sun yaba ma gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari bisa yin namijin kokari a ɓangaren ilimi.

Da suke tofa albarkacin bakinsu, wasu daga cikin ɗaliban makarantar Rahama Abdullahi, Rahanatu Ibrahim Birnin Kuka da kuma Fa’iza Tanimu Mashi sun bayyana jin daɗinsu ga gwamnatin jihar Katsina da kwamitin kula da makarantar bisa aiwatar da ayyukan AGILE a makarantar.

Inda suka yi nuni da cewa kayan koyar da sana’o’in hannun da aka samar za su taimaka masu wajen zama masu amfani a cikin al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *