September 17, 2026

A Cikin Watan Disambar Ne Za A Kammala Gadojin Kofar Ƙaura Da Kofar Ƙwaya A Katsina.

0

A cikin watan Disambar wannan shekarar ne za a kammala aikin gadar ƙasa da ke gudana a Kofar Kaura da Kofar Ƙwaya da ke cikin birnin Katsina.

Wakilin Kamfanin Triacta da ke gudanar da aikin Engineer Sadiq ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake zagayawa da gwamnan jihar Katsina a wuraren ayyukan 2 lokacin da ya kai ziyarar duba aikin.

Ya bada tabbacin cewa, zuwa sati mai kamawa ne za a fara shinfiɗa ma gadar Kofar Ƙaura kwalta.

Kamar yadda ya bayyana, za a rushe Kofar Ƙwaya domin aji daɗin yin ayyukan wurin.

Gwamna Aminu Bello Masari da ya bayyana gamsuwa da ingancin aikin da ya gane ma idonsa, ya yi fatan ganin an kammala aikin cikin lokaci.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *