September 18, 2026

Inaso Kafin Zaɓe Ba Wanda Zai Yi Saura Cikin Jami’yyar APC Katsina. -Yakubu Lado

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya bayyana cewa yana fatan kafin nan da lokacin zaɓe babu sauran wanda zai rage a jam’iyyar APC a Katsina.

Samata Yakubu ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala wata ziyarar ban girma da ya kaiwa tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustapha Inuwa a ofisoshin yakin neman zabensa.

Haka kuma ya ƙara da cewa fuskokin da suka bayyana a wannan ziyara da suka kai ta nuna irin yadda suka samu tarba a wannan ziyara.

Sanata Yakubu Lado ya ce Mustapha Inuwa yana da tunani na cigaban Katsina saboda haka yake son su haɗa hannu da shi wajan kafa gwamnati domin tunkarar matsalolin da suka addabi jama’ar jihar Katsina.

ɗan takarar ya ce duk wanda suka san cewa zai taimakawa tafiyarsu za su tuntuɓeshi domin ganin an haɗa karfi da ƙarfe wajan samun nasara zaɓe mai zuwa.

“Saboda haka sai na maida jami’yyar APC ta Katsina babu kowa kafin lokacin zaɓe ta hanyar tuntuɓa da tattaunawa da jama’a domin ganin an yi tafiya tare da kowa da kowa” inji

Kazalika ya ƙara da cewa yana da kyakkyawan shiri akan matsalar tsaro da ba zai bayyana ta a yanzu ba saboda dalilai na tsaro, amma dai idan ya samu nasara za a ga abinda zai yi.

“Kasan shi yaki ɗan zamba ne, ba zaka bayyanawa duniya shirin da kake da shi ba, musamman akan sha’anin tsaro, idan ka bayyana, kamar kana gayawa abokan faɗa cewa su ƙara shiri ke nan” inji shi.

Samata Yakubu ya faɗa cewa yana da tunanin sanyo masana a kowane ɓangare idan ya samu nasara domin su bada shawara akan yadda za a tafiyar da sha’anin al’umma musamman samar da sana’o’i ga matasa.

“Na sha faɗa cewa idan Allah ya ba mu nasara muka kafa gwamnati zan yi amfani da abokaina ‘yan kasuwa in jawo su zuwa Katsina domin kafa masana’antu don baiwa matasa aikin yi.” Inji Sanata

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *