September 17, 2026

An Bukaci Shugabannin Makarantun Jihar Katsina Su Sanya Gaskiya A Shirin AGILE.

0

An bukaci shuwagabanni makarantun sakandaren jihar Katsina su sanya gaskiya wajen aiwatar da shirin nan na AGILE a makarantunsu.

Shugaban kungiyar iyayen dalibai dana malamai da kuma na kwamitin kula da makarantu na makarantar sakandiren gwamnati ta Mahuta suka bada shawarar hakan a lokacin ziyarar duba ayyukan gyaran gine-ginen makarantar karkashin shirin AGILE.

Alhaji Magaji Bakarye da Alhaji Kabir Sani Mahuta sun bayyana shirin a matsayin wata hanya da za ta magance wasu matsalolin da makarantun sakandaren jihar ke fuskanta.

Sun kuma yaba da matakin da aka dauka na damka kula da shirin ga shuwagabanni makarantun don aiwatar da shi.

A jawabansu, shuwagabannin makarantun na sashen ƙarama da babbar sakandare Muhammad Abdulsalam da Malam Salisu Saulawa sun ce, an gyara makewayi tare da gina rijiyar burtsatse, hadi da sanya tankin adana ruwa mai cin lita dubu 5 a makarantar.

An kuma gyara rukunin gini mai ɗauke da azuzuwa 3 a bangaren karamar sakandare.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *