An Gargaɗi Jami’an Dake Kula Da Shirin Fadama Su Guji Amsar Kudin Goro Ga Manoma.
An gargadi jami’an dake kula shirin Fadama akan karbar na goro ga manoma a lokacin bada tallafin kayan gona na covid19 a jihar Katsina.
Babban jami’in kula da shirin na jahar Katsina Mas’udu Mustapha ya yi wannan gargadin a cikin sakon da ya aike ga manoman da aka zabo daga shiyyar Daura da Katsina domin amfana da shirin.
Babban jami’in wanda ya samu wakilcin jami’in yada labaran shirin na Fadama Lawal Abdu Kofar Sauri ya ce kayayyakin da ake rabawa kyauta wani kokari ne da rage radadin annobar covid19.
Ya ce an kirawo manoman ne zuwa Katsina ƙarƙashin shirin nan na fadama N-Cares don tabbatar da cewa manoman gaskiya ne aka ba kayan noman.
Kayan dai sun haɗa da takin zamani, injin feshin magani, maganin kashe kwari, da dai sauransu.
A jawabin godiya malam Na’ilu Daura da Hajiya A’isha Sani sun godema gwamnatin jiha bisa basu tallafin .
