September 17, 2026

Dikko Raɗɗa Ga Manoma: Ina Da Gurin Haɓaka Harkar Noma Da Kiwo A Jihar Katsina.

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa ya jaddada ƙudirinsa na taimakawa harkar noma da kiwo idan ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan a shekarar 2023.

Dakta Umar Raɗɗa ya bayyana haka a lokacin wani gangami da ƙungiyar manoma ta jihar Katsina (AFAN ) ta shirya domin nuna goyon bayan ‘ya ‘yan kungiyar akan tafiyar siyasar.

Dikko Raɗɗa ya cigaba da cewa babbar matsalar da addabi harkar noma da kiwo a jihar Katsina ita ce matsalar tsaro wanda ya ce zai iyakar ƙoƙarin sa wajan ganin manoma sun dawo da martabar Katsina ta fuskar noma da kiwo

“idan Allah ya bani nasara zai dawo da tsari nan na ma’aikatar gona, wanda aka sani tun da can, na masu koyawa manoma dubarun noma na zamani da zai ƙara inganta hanyoyin noma da kiwo a kimiyance” inji shi

Dakta Dilkko Raɗɗa yana mai cewa dukkan abinda zaka ba manomi na tallafi madamar baka nuna ma shi yadda zai amfani da shi ba, to baka taimake shi ba, saboda haka a matsayin shi na wanda ya yi babban digiri akan noma ya zama wajibi ya ba shi mahimmanci

A jawabinsa shugaban kungiyar manoma ta jihar Katsina Hon. Yau Umar Gwajo-gwajo ya nuna bukatar da ake da ita ga ɗan takarar gwamna da yasa Noma da kiwo cikin abubuwan da zai ba mahimmanci.

Hon. Yau Umar Gwajo-gwajo ya ƙara da cewa kungiyar manoma ta jihar Katsina a shirya take wajan mara masa baya domin ganin ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina da za ayi a shekarar 2023.

“Muna son idan Allah ya ba Dikko Umar Raɗɗa nasara ya dubi manoma da idanun basira wajan tallafa masu da abubuwan da suke buƙatar na zamani da za su ƙara inganta harkar noma da kiwo a jihar Katsina baƙi ɗaya” inji shi

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *