Masu Zuba Jari Na Kasar Sin Za Su Noma Hekta 10,000 Ta Shinkafa A Yobe – Buni.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a jiya Laraba ya ce kungiyar masu zuba jari na kasar Sin za su kafa gonakin noman hekta 10,000 a karkashin wani shirin noma a jihar.
Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shi Mamman Mohammed ya fitar a Damaturu, lokacin da kungiyar ta kai mashi ziyarar ban girma.
Ya bayyana shirin gwamnatin sa na hada hannu da masu zuba jarin domin bunkasa noma a jihar.
Ya ce “A shirye muke mu hada kai don haka ya kamata mu yi amfani da damar noman.”
Buni ya bayyana cewa, zasu ci gaba da ba noma fifi dake zama babbar sana’ar jihar.
Ya kuma bukaci jama’a da su yi amfani da wannan damar domin samun abin dogaro da kai da kuma inganta noman jihar.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Mr. Yung Wang, ya ce zuba jari a fannin noma na jihar zai bunkasa samar da abinci da kuma taimakawa wajen bunkasar tattalin arziki, inji majiyar Popular News Hausa Hausa ta jaridar Vanguard.
Ya bayyana cewa kungiyar za ta shuka shinkafa mai yawan gaske a jihar.
Ya ce, “Irin zai samar da adadin shinkafar sau biyar da ake noma yar gida.
Wang ya ce, “suna sauya fasahar noma zuwa ta zamani irin wadda ake aiki da ita a kasar China.”
