September 17, 2026

An Kaddamar Sabon Kamfanin Kiwon Lafiya Mai Suna Al-Inaya Hijama Basic Services A Jihar Katsina.

0

A lokacin da yake jawabin kaddamar da kamfanin, shugaban kamfanin Aminu Yusuf Mamman D ya ce sun buɗe shi ne a jihar Katsina domin kishin al’umma.

Ya bayyana cewa, kamfanin za ya gudanar da ayyukan mako ɗaya cikin farashi mai sauki daga wannan Juma’ar 09/09/2022 zuwa Juma’a mai zuwa 16/09/2022.

Kamar yadda ya bayyana, sun tanadi ingantattun kayan aiki na zamani domin yin aune-aune da kuma aiki ga marasa lafiya.

Kamfanin mai suna Al-Inaya Hijama Basic Services nada sashen auna marasa lafiya, sashen yi masu aiki, tare da na basu magani.

Jami’an kamfanin sun gwada ma yan jarida da sauran al’umma iri yadda suke ayyukan kiwon lafiyarsu cikin tsafta.

Cututtukan da kamfanin ke bada maganinsu sun haɗa da farar masassara, ciwon suga, ciwon iska, gyanbon cikin matsalar sanyi, yoyon fitsari da kuma ciwon hanta.

Sauran sun hada da zafin jiki, masassarar hanji, tarin TB, tarin huka da kuma hawan jini.

Ciwon baya, ciwon kafa, ciwon kai, ciwon kugu, basir da kuma ciwon kunne dana ido.

Kamfanin nada ofishi akan titin Yahaya Madaki, Shataletalen Makarantar Kiddies, tsallaken gidan man Kokiya, saman bene, cikin garin Katsina.

Ko kuma a tuntube su ta lambar waya kamar haka: 07066200123, ko kuma 07058086728.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *