September 17, 2026

Rundunar Sojoji ta kori Sojojin Da Suka Kashe Sheikh Goni Aisami Gashuwa

0

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana daukar matakin korar wasu sojojinta biyu bisa samun su da laifin aikata kisan kisan wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a jihar Yobe.

Wadannan sojojin da aka kora sun hada da Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.

Sanarwar korar ya fito ne daga mukaddashin kwamandan da ke kula da Bataliya ta 241 dake Nguru a jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, inda ya shaida wa manema labarai cewa kwamitin binciken hadin gwiwa da aka kafa tare da hadin gwiwar yan-sanda ya same su da laifi.

Ya kara da cewa an sallami wadannan sojojin biyu ne saboda tuhume-tuhume guda biyu da aka same su dasu; na rashin yin ayyuka bisa ka’ida da kuma nuna kyama ga horon da suka samu na gidan soji.

Bugu da kari kuma, Laftanar Kanar Osabo ya ce za a mika wadannan sojojin da aka kora ga hannun yan- sanda a jihar Yobe domin gurfanar da su a gaban kotu bisa laifukan da suka aikata.

A makon da ya gabata ne wadannan sojojin suka yi wa Sheikh Goni Aisami Gashuwa kisan gilla kusa da garin Jaji-maji, shalkwatar karamar hukumar Karasuwa, a kan hanyarsa daga Kano zuwa gida Gashuwa.

Al’ummar gari hadi da yan -sanda a Jaji-maji ne suka samu nasarar kama sojojin wanda daga bisani aka gabatar da su a ranar 23 ga watan Agustan 2022, da ake zargi da hannu a kisan Malamin.

Mai magana da yawun Rundunar Yan-sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, a wata zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce sun kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47.

Haka kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan inda kuma ya bukaci a gaggauta hukunta sojojin da suka aikata kisan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *