Rawar Da Na Taka A Cikin Fim Ɗin “Zo Mu Zauna” Ba Halina Bane . Cewar Jaruma Amina A Shehu
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Sabuwar jaruma a Masana’antar Kannywood Amina A Shehu wadda ta fito a matsayin Nadiya a cikin shiri mai dogon zango mai suna Zo Mu Zauna ta bayyana cewar fim ɗin Zo Mu Zauna wani fim ne da take jin sa a ranta saboda yadda fim ɗin ya ɗaukaka darajarta.
Jarumar wadda ta ce ta yi finafinai masu yawa a baya kamar Gidan Danja sai dai a wannan fim ɗin na Zo Mu Zauna ta ji daɗin yadda ta fito a cikin Jaruman fim ɗin.
Haka kuma jarumar ta ce yadda ta fito a matsayin ‘yar shagwaba a fim ɗin wadda iyayen ta suka nuna mata gata take yin abin da take so sai wasu su ke ganin kamar halin ta ne, kuma ba haka ba ne, fim ɗin ne ya zo da haka domin tana bin rol ɗin da aka ba ta ne a matsayin jarumar da take neman kwarewa, kuma hakan yake nuna jarumi ya san aikin sa.
Amina Shehu ta ƙara da cewa babbar Matsalar da jarumai suke fuskanta, shi ne yadda mutane su ke kallon su a matsayin wasu mutane na daban, domin ka ga ko a gidan mu har yanzu ƙanin Babana bai amince da abin da nake yi ba a matsayin sana’a nake yi, kodayake mahaifiyata ta amince ‘yan uwana sun amince, shi ne dai kawai bai gama amincewa ba.
To Amma ita a cewar. Komai nufin Allah ne duk abin da Allah ya ƙaddara za ka yi ba ka da tsumi ba ka da dibara sai ka yi shi.
Daga karshe ta yi kira ga masu kallon finafinai da su rinƙa yi musu kallon mutane kamar kowa, yadda a ke kallon ta a matsayin Nadiya a cikin shirin Zo Mu Zauna, ta yi ne a matsayin da aka ɗora ta domin ta faɗakar da masu irin wannan halin da su ma iyayen da su ke ɗora ya’yan su a kan irin wannan matakin.
