September 17, 2026

Za a Rantsar Da Daraktan Finafinai Hausa A Matsayin Alkalin Shari’ar Muslunci A Katsina

0

Idan Allah mai kowa mai komi ya kaimu a ranar talata 11/10/2022 da misalin karfe 9am na safe.

Za’a rantsar da Alkali Jamilu Abdullahi (Mj Saulawa) a matsayin Alkali, kuma daya daga cikin alkalan kotun Shari’ar musulunci.

Za’ayi wannan rantsuwa ne a babban dakin taro na High Court dake a cikin birnin katsina.

Wannan yana a matsayin goron gayyata ga “yan’uwa da abokan Arziki.

Allah ya bada ikon halarta Amin.

MJ saulawa na daga cikin manyan manyan daraktocin Kannywood a nan jihar Katsina kuma shine daraktan kamfanin Blue sounds da sauran kamfanoni shirya finafinai a nan Katsina

haka kuma shine ya bada umarnin a finafinan kamar su; Ba Duhu da Ya-Na -Iya da Alaƙaƙai da Raliya da Ɗan Ba da sauran su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *