September 17, 2026

Kotun Daukaka Kara Ta Umurci Kungiyar ASUU Ta Koma Bakin Aiki.

0

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, ta umarci kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shiga cikin gaggawa.

Kotun daukaka karar ta bayyana cewa, janye yajin aikin shi ne kawai sharadin bukatar kungiyar ta neman daukaka karar hukuncin kotun masana’antu ta Najeriya.

Bayan tattaunawa dai, gwamnatin tarayya ta kai kungiyar ASUU zuwa kotun masana’antu ta kasa, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta DailyTrust.

A hukuncin da ya yanke a ranar 21 ga Satumba, 2022, Mai shari’a Polycarp Hamman, alkalin kotun masana’antun, ya umurci malaman da ke yajin aikin da su ci gaba da aiki cikin gaggawa har sai an warware takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnati.

Alkalin ya ce sashe na 18 na dokar takaddamar ciniki da ya ba shi ikon yanke irin wadannan shawarwarin domin amfanin al’umma.

Jami’ar ba ta gamsu ba, ta shigar da kara domin kalubalantar umarnin kotun masana’antun. Kuma kotun daukaka kara ta shawarci gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago da su sasanta lamarin da tsakaninsu.

Sai dai a ranar Alhamis da za a ci gaba da sauraren karar, lauyan kungiyar ASUU, Femi Falana (SAN), ya shaida wa kotun daukaka kara cewa bangarorin biyu ba za su iya warware yajin aikin da aka shafe watanni takwas ana yi ba a kotu.

James Igwe, lauyan gwamnatin tarayya, ya kuma shaidawa kotun daukaka karar cewa duk da shawarar da aka basu, ba za su iya warware rikicin ba.

A hukuncin da aka yanke wannan Juma’ar alkalin kotun, Mai shari’a Hamma Barka, ya umarci malaman da su koma bakin aiki cikin gaggawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *