September 17, 2026

Yajin Aikin ASUU: Dalibar Shari’a Ta Nemi Kotu Ta Tsaida Da Albashin Buhari.

0

Rikicin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta ASUU ya sa wata dalibar lauya da ke shekarar karshe mai suna Soohemba Agatha Aker shigar da karar, inda ta bukaci kotu ta dakatar da biyan albashi da alawus-alawus din shugaba Mohammadu Buhari, Gwamnonin Jihohi 36, dama sauran masu rike da mukaman siyasa a kasar nan har sai an cimma matsayar kawo karshen yajin aikin ASUU a Najeriya, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Sunnews.

Dalibar ta Jami’ar Jihar Benue, Markudi, tana neman ayi hakan ne a kan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Sakataren Gwamnati, Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai, Ministoci, Manyan Sakatarorin gwamnati, Shugabannin Hukumomi da dai sauransu.

A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1684/2022, ta bayyana cewa a halin yanzu yajin aikin ya shafe ta, saboda haka ta shigar da karar a madadin daukacin daliban manyan makarantun gwamnati.

A karar da lauyan ta Chukwuma-Machukwu Ume SAN ya shigar ta bayyana sunayen wadanda ake karan da suka hada da gwamnatin tarayyar Najeriya, kungiyar malaman jami’o’i, shugaban majalisar dattawan Najeriya, shugaban majalisar wakilan Najeriya da kuma Gwamnan jihar Abia (wadda za ta tsaya a madadin sauran jihohin Najeriya).

Sauran su ne hukumar rabon arzukin kasa; kwamitin kula da rarraba kudin asusun gwamnatin tarayya; ministan shari’ar Najeriya; babban atoni na jihar Abia (wanda za a tuhuma a matsayin wakili na sauran jihohi 35 na Tarayya); mataimakin shugaban jami’ar Abuja (a matsayin wakilin sauran mataimakan shugabannin jami’o’in Najeriya da na jihohi) da Umar Faruk shugaban kungiyar daliban Najeriya.

An shigar da karar ne bisa ga sashe na 46 (1), (2) da (3) na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma sashe na 17(1) na Yarjejeniya Ta Afirka kan Hakkokin Dan Adam (Tabbatarwa da Taimakawa) Dokar Babi A9 (Charter 10 LFN). 1990) Na 2, 1983.

Hakanan kuma mai shigar da karar ta bukaci a tilasta wa wadanda ake tuhuma da suka hada da hukumar gudanarwar jami’o’in da ke yajin aiki da su mayar da albashi da alawus-alawus baki daya da suka amsa tun daga ranar da aka fara yajin aikin har ya zuwa yanzu, kafin a ci gaba da sauraron karar.

Ta kuma bukaci a ba da umarnin dakatar da ayyukan wanda ake kara na 6 da 7 (hukumar rabon daunin arzukin kasa da Kwamitin kula da rarraba kudin asusun gwamnatin tarayya) da suka hada da biyan kudaden kason kowane wata ga wadanda ake tuhuma na 3, 4, 5, 8, 9 da 10 har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

A cikin takardar goyon bayanta, ta ce yajin aikin ASUU ya ci tura kuma yana ci gaba da yi mata illa ga batun kammala karatunta a wannan shekarar ta 2022 balle ta shiga makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya

Ta ce wannan shekarar karatun za ta tafi a banza ba a yi komai ba.

Ta kara da cewa burinta na kammala karatun lauya na gab da rugujewa domin mai daukar nauyinta ya bayyana cewa, bana ita ce shekarar karshe da ya dauki nauyin karatun ta a makaranta.

Ta bayyana cewa abokan karatunta ‘ya’yan masu hali ne, saboda haka suke ta maida karatunsu a jami’o’i masu zaman kansu na kasar nan ko kuma a kasashen waje.

Cewa wasu daga cikin ma’auratan sun samu ciki saboda gajiya da zaman banza.

Ta ce, tana fama da matsananciyar damuwa a kowace rana saboda ci gaba da yajin aikin ba tare da wani takamaimen matakin da masu ruwa da tsaki suka dauka na kawo karshensa ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *