An kama Wasu Daga Cikin Maharan Cocin Garin Owo Dake Ondo.
An kama wasu mutane biyu daga cikin wadanda suka kitsa harin ta’addancin da aka kai a cocin St. Francis Catholic dake Owo, jihar Ondo a Kudu maso yammacin Najeriya. Wadanda ake zargin da aka bayyana a matsayin manyan kwamandojin ISWAP a Najeriya, su ne Idris Ojo mai shekaru 32 da Jimoh Ibrahim mai shekaru 39, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta AIT.
Babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor wanda ya bayyana hakan ga manyan Editoci a wani taron jama’a a yau Talata a Abuja, ya ce an kama mutanen biyu ne a wani samame na hadin gwiwa na tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da jami’an DSS.
Janar Irabor ya ce an kama Idris Ojo ne a Ayetoro dake jihar Ondo a ranar Lahadi 7 ga watan Agusta tare da wasu kwamandojinsa, wadanda tuni suke shirin kai wani hari kafin bayanan sirri su nuna inda yake, kuma daga bisani aka kama shi a samamen da aka kai wurin.
Babban hafsan hafsoshin tsaron ya ce an kama wasu mutane hudu a Eja dake karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi, dangane da harin da aka kai cocin Katolika a garin Owo a ranar 5 ga watan Yuni da kuma wani harin da aka kai ofishin ‘yan sanda a Ada inda aka kashe dan sanda.
Babban hafsan hafsoshin tsaron ya ce duk wadanda aka kaman a matsayin manyan ‘yan kungiyar ISWAP a Najeriya nan ba da jimawa ba za a gabatar da su a bainar jama’a. Janar Irabor ya ce ana ci gaba da gudanar da gagarumin aiki a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya domin yakar ‘yan bindiga, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.
