September 18, 2026

Rashin Tsaro: Za Mu Ceto Jihar Zamfara Daga Hannun ‘Yan ta’adda – Atiku.

0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya tabbatar wa al’ummar jihar Zamfara cewa, “ yana kan hanyar ceto su,” daga rashin tsaron da yankin yake ciki.

Atiku ya ce zai yi kokarin ganin dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP, Dr. Dauda Lawal ya lashe zaben shekarar 2023 dake tafe, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Sunnews.

Wata sanarwar manema labarai daga ofishin yakin neman zaben Daudu Lawal dake Gusua ta ce Atiku ya fadi hakan ne a ranar Laraba lokacin da dan takarar PDP ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban kasar a gidansa da ke Abuja.

Sanarwar ta ruwaito Atiku na cewa hanyar ceto da sake gina Zamfara ita ce raba jam’iyyar APC da mulki a shekarar 2023.

Sanarwar ta ce, “domin cimma hakan, akwai bukatar samun hadin kan jam’iyyar PDP wanda hakan zai ba ta damar cimma abubuwan data sanya gaba.

Ya ce “abin da ya fi dacewa a yi wa al’ummar Jihar Zamfara shi ne a samar da zaman lafiya don ganin suna zuwa gonakai da yin harkokin kasuwanci.

“Amma halin da ake ciki yanzu ba haka yake ba. Dole ne mu cire jam’iyar APC daga mulki don cetowa da kuma sake gina jihar dama kasa baki daya. Haka kuma gwamnatin ta PDP za ta farfado da masana’antar masaku.

“Tun da farko, saida Dauda​wanda​tsohon Babban Daraktan Bankin First Bank ne ya bayyana cewa, ya jagoranci masu ruwa da tsaki na PDP da jiga-jigan APC da suka sauya sheka zuwa PDP, domin taya Atiku murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar.

“Lawal ya bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan Najeriya a yanzu sun gamsu da jam’iyyar PDP saboda sun dandana kudar su hannun jam’iyar APC.

Shigowar wadannan jiga-jigan wani babban ci gaba ne ga jam’iyar PDP a jihar ta Zamfara, idan aka yi la’akari da matsayi, hadi da kimar a cikin jam’iyar APC.

Daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara da Atiku Abubakar ya karba akwai Alhaji Salihu Mai Buhu Gummi, Alhaji Sahabi Liman Kaura, Alhaji Illili Bakura, Engr. Garba Ahmad Yandi, Hon. Ikra Bilbis, Dr. Na’Allah Isa Mayana, Hon. Mukhtar Lugga, da sauransu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *