September 18, 2026

Ana Muzgunawa Yarana A Jam’iyyar APC ta Katsina – Dakta Mustapha Inuwa

0

Daga Abu Ahmad, Katsina

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka yi takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyar APC bai samu nasara ba, Dakta Mustapha Inuwa ya ce yanzu an sanyo yaransu gaba a jam’iyyar APC ta jihar Katsina

Dakta Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne a lokacin wata hira da ya yi da kafar BBC Hausa inda ya yi zargin yadda ake neman maida shi yaranshi da shi kanshi saniyar ware a jam’iyyar APC

Ya kuma bayyana cewa tun bayan kammala zaɓen fidda gwani bai sake jin wani bayani daga wajan jam’iyyar ba, in banda bita da kulli da ake yi wa duk wanda aka san yana tare da shi.

“Yanzu ba abinda ake yi sai tsangwamar duk wanda aka san yana tare da mu, wasu ma an kore su, sannan ban san halin da ake ciki ba game da jam’iyyar APC a jihar Katsina.” In ji shi

Sai dai da yake maida martani game da wadancan zarge-zarge da Dakta Mustapha Inuwa ya yi matamakin shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abu Musawa ya ce jam’iyyar su ta APC dunkule take uwa ɗaya uba ɗaya.

Ya ƙara da cewa tun bayan da aka kammala zaɓen fidda gwani babu wani taro da jam’iyyar APC ta yi, amma dai ta kira taron sasanshi da ban hakuri inda aka gayyaci Dakta Mustapha Inuwa.

” Tun bayan wannan lokacin ban sake jin wata sa toka sa katsi daga wajan tsohon sakataran gwamnatin jihar Katsina ba har zuwa yanzu” inji Bala Abu Musawa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *