September 19, 2026

Zaɓen 2023: Matasan Arewacin Yobe Suna Goyon Bayan Hon. Bashir Machina

0

Daga Muhammad Maitela, Yobe

Gamayyar kungiyar matasan Arewacin Yobe, ‘Yobe North Youths Alliance’ ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga Ɗan takarar majalisar dattawan Najeriya, wanda ya kunshi ƙananan hukumomin Bade, Jakusko, Yusufari, Karasuwa, Nguru da Machina, Hon. Bashir Machina. Tare da bayyana cewa sun ɗauki matakin bayan tuntuɓar ilahirin matasan yankin tare da cancantar sa da gogewa a siyasa da mu’amala.

A zantawar wakilinmu da Kwamared Muhammad Nura Gashuwa, bayan rangandin da kungiyar ta gudanar a yankin, tare da tuntuɓar kowane ɓangare. Ya ce matasan sun cimma wannan matsayar ne baya ga la’akari da suka yi da nagartar Hon. Machina wanda suka ce ko shakka babu zai yi wa yankin wakilci nagari a zauren majalisar dattawan Najeriya, idan ya samu amincewar al’ummar Arewacin Yobe.

“Wannan yanki na Arewacin Yobe ya na buƙatar mutum irin Hon. Bashir Machina saboda gogewar sa a harkokin siyasa tare da mu’amala da jama’a. Sannan kuma mutum ne mai sauraren ra’ayoyin jama’a, ƙyakkyawar fahimta da girmama kowa da kowa. An san shi da kwatanta gaskiya da rikon amana, kuma mutum ne mai kwazo kuma karɓaɓɓe a gun kowa.” In ji shi.

“Al’ummar wannan yankin shaida ne dangane da ayyukan ci gaba da ya samar wa wannan jihar baki ɗaya, tsawon lokacin da ya zauna a hukumar kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya, kana kuma ya samar wa matasa ayyukan yi, tallafin karatu da makamantan su, wanda muke ganin idan jama’a suka bashi dama zai kawo ci gaba mai ma’ana a Arewacin Yobe.”

Muhammad Nura ya ƙara da cewa, “Idan an kalli gwagwarmaya da faɗi-tashi a fannin siyasa, Hon. Bashir Machina kwararre ne kuma ya yi an gani, saboda yadda ya kawo ci gaba mai dimbin yawa ba a yankin sa kadai ba, ilahirin jihar Yobe an ci gajiyar sa.”

“Saboda haka muna kira ga baki ɗayan al’ummar ƙananan hukumomin Arewacin Yobe shida (6) su bai wa Hon. Bashir Machina goyon baya, su zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar dattawa, domin samun ci gaba mai ma’ana.” Ta bakin Alh. Nura.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *